Home Back

Ali Nuhu Ya Gabatar Da Lacca Kan Fina-finan Nijeriya A Faransa

leadership.ng 2024/6/26
Ali nuhu

Shugaban hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu ya gabatar da wata lacca a lokacin da ya halarci wani taro kan yadda fina-finan Nijeriya za su samu damar shiga kasashen duniya.

Taron wanda manyan masu ruwa da tsaki suka tabo batutuwa da sauran hanyoyin da za a bi wajen shigar da fina-finan Nijeriya lungu da sakon kasashen duniya.

Manyan mutane daga Nijeriya da suka halarci wannan taro sun hada da tsohon ministan al’adu da yada labarai a lokacin mulkin shugaba, Muhammadu Buhari, Lai Muhammad, shugabar kwamitin bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar fasaha da basirar zamani, Rahama Sadau da sauran manyan masu ruwa da tsaki a harkar fim a Nijeriya.

A wani rubutu da Ali Nuhu ya yi a shafinsa na sada zumunta na Facebook, an hango jarumin yana cewa, “Na gabatar da lacca a taron fina-finan Nijeriya na kasa da kasa a Cannes na kasar Faransa. Hankalina kacokan ya koma kan taken “Global Outreach for Nigerian Films: Opportunities and Limitations.”(Shigar Fina-finan Nijeriya zuwa kasashen duniya akwai damarmaki da kalubale).

“Na nuna karuwar sha’awar duniya game da labaru daban-daban, habakar ilimin zamani na dijital da muhimmancin hadin gwiwa tare da masu shirya fina-finai na duniya, wanda haka ne kadai zai zamto kamar wata hanya ta shigar da fina-finan da ake shiryawa daga kasashen duniya zuwa ko’ins cikin sauki.

“Haka zalika, na tabo batun kalubalen da wannan yunkuri yake fuskanta da suka hada da karancin kudi, kayan aiki da kuma tallace-tallace da hanyoyin da za a bi wajen magance dukkan wadannan abubuwa a saukake.

“Ma’aikatar al’adu da kirkir-kirkire tana aiki tukuru don samar da tallafin kudi da kuma inganta hanyoyi da cibiyoyin kasuwanci kamar hada hannu dan manyan kamfanonin zuba jari irinsu ‘Afredimbank’ da sauransu wajen tallafa wa da dawo da martabar manyan masana’antun shirya fina-finai da suke neman durkushewa, inda muke fatan yin duk abin da ya dace kafin wani taron na NIFS da za a gudanar a wannan shekarar ta 2024 a Birnin Cannes.”

Ali Nuhu shi ne shugaban hukumar Fina-finai ta Nijeriya, wanda Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada a farko wannan shekarar ta 2024. Tun bayan nadin nasa jarumin yake nemo hanyoyin da wannan hukuma za ta bunkasa harkar shirya fina-finai a Nijeriya.

Inda zuwa yanzu ya halarci manyan taruka a ciki da wajen Nijeriya domin zakulo hanyoyin da masana’antun shirya fina-finai a Nijeriya za su yi gogayya da takwarorinsu na kasashen duniya ta hanyar kwarewa, ci gaba da kuma kayan aiki irin na zamani, wanda hakan zai sa su dinga shirya manyan fina-finan da za a yi alfahari da su har watakila su samu kyaututtuka kamar na Oscar da makamantansu.

People are also reading