Home Back

Majalisa Ta Fadi Matakin Dauka Idan Tinubu Ya Bukaci a Siyo Masa Jirgi

legit.ng 3 days ago

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta ce babu wata barazana da za ta hana ta amincewa da buƙatar sayen jirgi ga shugaban ƙasaidan hakan ta taso.

Majalisar dattawan ta kuma bayyana cewa babu wata buƙatar neman a siyawa shugaban ƙasa Bola Tinubu jirgi da aka gabatar a gabanta.

Majalisa za ta amince da bukatar Tinubu kan siyo jirgi
Tinubu bai gabatar da bukatar siyan jirgi a gaban majalisa ba Hoto: Godswill Obot Akpabio, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a zauren majalisar dattawa a ranar Alhamis lokacin da ya yi ƙarin haske kan batun siyan jirgin, cewar rahoton jaridar The Punch.

"Mun damu da shugaban ƙasa kuma mun damu da al’ummar Najeriya. Za mu amince da abubuwan da za su amfani al’ummar Najeriya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu amince da abubuwan da za su inganta rayuwar jama'a. Har ila yau, za mu duba muhimmancin ayyukan shugaban ƙasa."
"Idan motarsa ta lalace, za mu gyara motar. Idan jirginsa ya lalace, za mu amince da kuɗin da za a yi gyaran jirgin. Domin haka wannan ba wani abu ba ne. Babu wani abu da aka gabatar a gabanmu."
"Ba na tunanin wannan wani abu ne da ya kamata ku damu da shi."

- Sanata Godswill Akpabio

Asali: Legit.ng

People are also reading