Home Back

Lalurar da ke sanya mutum maye ba tare da shan barasa ba

bbc.com 2024/6/26

Asalin hoton, Courtesy of Ray Lewis

Labradoodle Mia (dama) kan taimaka wa Ray Lewis kula da larurarsa ta buguwa
Bayanan hoto, Karya Labradoodle Mia (tsakiya) kan taimaka wa Ray Lewis (hagu) kula da larurarsa ta buguwa

A kwanan nan wani ɗan ƙasar Belgium ya ja hankalin mutane bayan kotu ta wanke shi daga zargin yin tuƙi cikin maye.

Bisa taimakon likitoci, an gano mutumin mai shekara 40 na da wata larura da ke sa mutum maye da ake kira auto-brewery syndrome (ABS), inda jikin mutum ke samar da barasa da kansa.

Mece ce wannan larura ta ABS? Kuma ta yaya mutumin ke rayuwa da ita?

Ray Lewis na sane da abu biyu lokacin da ya farka a gadon asibiti a Oregon da ke Amurka. Na farko shi ne batun hatsarin da ya yi da wata mota mai ɗauke da kifi 11,000 ta hukumar kula da kifaye da dabbobi, inda yake aiki.

Na biyu kuma, duk da cewa 'yansanda sun rubuta cewa akwai sinadarin kayan maye mai yawa a cikin jininsa, bai sha komai ba a daren da lamarin ya faru a Disamban 2014.

"Tabbas ban taɓa wata kwalabar giya ba saboda na san ina da balaguron awa biyu a mota," a cewar mutumin mai shekara 54.

Wata takwas bayan afkuwar hatsarin, an gano mutumin, wanda ƙwararre ne a harkar rayuwar halittu na fama ne da lalurar ABS wadda ke sa jikinsa ya riƙa samar da sanadari mai sanya mutum maye.

(Wani hoto da gidan talabijin na Amurka Fox 13 Seattle ya wallafa na nuna abin da ya biyo bayan hatsarin da Ray ya yi a 2014.)

Mece ce larurar ABS?

Larurar ABS ko kuma gut fermentation syndrome (GFS), yanayi ne da bai yawaita ba, wanda ke ƙara yawan sinadarin alcohol (mai sa maye) a cikin jinin mutum, wanda zai jawo maye ko da kuwa mai fama da ita bai sha giya ba.

Tana faruwa ne lokacin da ƙwayar cutar bacteria a hanjin mutum, ko hanyar fitsari, ko baki ta mayar da abinci da sikarin da ya ci zuwa sinadarin alcohol - abin da ake kira endogenous alcohol production a Turance.

Takan sa mutum ya koma maganar ƴan maye, da tangaɗi, da kuma barci maras kan gado.

Microscope picture of the fungus Saccharomyces cerevisiae

Asalin hoton, Getty Images

Wa take shafa?

ABS ba sananniyar cuta ce. Wani bincike da aka wallafa a 2021 a mujallar American Journal of Gastroenterology ya gano cewa mutanen da suka kamu da ita ba su wuce 100 ba Amurka, duk da cewa wasu na ganin ba a bayar da rahotonta yadda ya kamata.

Har yanzu likitoci ba su da tabbas game da dalilin da ya sa take shafar mutane.

An san cewa jikin ɗan'adam kan samar da sindarin alcohol kaɗan domin taimakawa wajen narkar da abinci. Amma a jikin mutane da dama, yakan lalace tun kafin ya shiga cikin jini.

"Dukkanmu mukan samar da sinadarin alcohol da kanmu, amma mai ABS kan samar da alcohol ɗin mafi yawa wanda kan je har cikin jini," kamar yadda Dr Ricardo Jorge Dinis-Oliveira ya yi bayani bayan ya wallafa maƙaloli da yawa a kan larurar.

Asalin hoton, Getty Images

Masu larurar ABS akasari kan gano matsalarsu ne bayan gwaji ya nuna ba su cikin hayyacinsu
Bayanan hoto, Masu larurar ABS akasari kan gano matsalarsu ne bayan gwaji ya nuna ba su cikin hayyacinsu

"Abin haushi, yawanci sai an tuhumi mutum a kotu kafin su iya sanin suna ɗauke da lalurar."

Ya siffanta ABS da "babbar guguwa a fannin narkar da abinci" - ma'ana akwai abubuwa da yawa da ke haifar da ita a lokaci guda. Na farko shi ne samuwar cutuka kamar ciwon suga, teɓa da sauran su.

Na biyu kuma kan shafi magungunan da masu lalurar kan sha, kamar masu kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics) da immunosuppressants waɗanda ke shafar wani sashen hanji.

Rayuwa da ABS

Lokacin da ma'aikacin jinya a Amurka Joe Cordell ya fara magana irin ta ƴan maye yayin wata liyafa tare da danginsa, ya zaci naman da ya ci ne ya yi yawa.

Sai kuma wani abokin aikinsa a asibiitn Texas ya zarge shi da shan giya yayin aiki - wanda laifi ne da ke iya janyo hukuncin kora daga aiki.

"Sun ce numfashina na warin giya," a cewar Cordel mai shekara 75. "Mutane sun zaci mashayi ne ni.

"Na ji kunya sosai saboda ina cikin mutanen da ke ƙaunar aikinsu sosai kuma ban taɓa fashin zuwa ba ko sau ɗaya."

Asalin hoton, Courtesy of Barbara Cordell

Barbara Cordell ta zama mai faɗakarwa kan ABS bayan mijinta Joe ya kamu da larurar
Bayanan hoto, Barbara Cordell ta zama mai faɗakarwa kan ABS bayan mijinta Joe ya kamu da larurar

Matarsa ma mai suna Barbara ta yi zargin yana shaye-shaye ne.

"Ban yarda da Joe ba da farko," in ji ta. "Na saka wa kwalaban da muka sha alama kuma na duba don tabbatar da cewa ba a jirkita su ba."

Asalin hoton, Getty Images

A pizza topped with french fries
Bayanan hoto, Rage cin abinci nau'in carbohydrates zai iya taimakawa wajen rage ABS

An gano Joe na ɗauke da ABS a 2010, shekara ke nan bayan ya ji alamun cutar. Ya ci gaba da yin aiki a hakan amma kullum sai an yi masa gwajin barasa.

Hakan ya Barbara ta kafa wata ƙungiyar tallafa wa masu larurar, wadda ke da mambobi kusan 850.

"Mukan saurari marasa lafiya a kullum da likitoci ba su sauraron su yadda ya kamata," in ji ta.

"Abin haushin ma sai a yi ta tsangwamar su, ana kunyata su, ana ƙaryata su, a zarge su da ƙirƙirar cuta kuma ba a ba su kulawar da ta dace."

Ta ce a ƙarshe ma hakan kan sa "su haƙura kuma su koma shaye-shayen da gaske don rage wa kan su raɗaɗi".

Ta yaya ake gane ABS kuma kuma ta yaya ake kula da ita?

Da farko likitoci kan kore alamun cutar. Daga kuma ƙila su gudanar da gwaji don ganin ko akwai ƙwayar cutar bacteria a hanyoyin narkar da abinci.

Wani zubin kuma sukan yi gwajin glucose inda za a nemi maras lafiya ya ci abinci mai yawan carbohydrate, ko kuma ya ci glucose ɗin kafin ya ci komai. Bayan 'yan awanni, mutane da ba su da larurar za a ga ba su da sinadarin alcohol a cikin jininsu, masu ita kuma za a gan su da shi mai yawa.

Asalin hoton, Courtesy of Ray Lewis

An bai wa karyar Mia the Labradoodle horon yadda za ta gano sauyi a jikin Ray, shi ya sa yake yawo da ita zuwa ko'in
Bayanan hoto, An bai wa karyar Mia the Labradoodle horon yadda za ta gano sauyi a jikin Ray, shi ya sa yake yawo da ita zuwa ko'in

Ray ya samu yadda zai rage girman lalurarsa ta hanyar ɗaukar hayar karya mai suna Mia.

An ba ta horo yadda za ta sansano sauyin sinadaran da ke jikin Ray, ciki har da yawan sinadarin maye. Idan ta gano wani sauyi, sai ta tsaya a gabansa ta ƙura masa ido.

"Kafin na samu Mia kodayaushe ina cikin fargabar wani abu zai iya faruwa da ni ko sauran mutane," in ji Ray.

"Loakcin da na yi hatsari, abin da na fi jin daɗi shi ne ni kaɗai na ji rauni kuma ban buge kowa ba."

People toasting with glasses of beer

Asalin hoton, Getty Images

Ba kamar sauran mutane ba da ake ƙyalewa idan gwaji ya nuna sun koma hayyacinsu bayan kama su da laifin tuƙi cikin maye, Ray bai yi sa'a ba.

"Alƙalin ya fahimci matsalar dai tawa ce ko ma ta yaya aka yi giya ta shiga jikina," a cewarsa.

"Ina da larura kuma duk da hukuncin kotu, abin da ya rage min kawia shi ne na nemi haƙƙina."

Shi da matarsa Sierra na ƙoƙarin ɗaukaka ƙarar hukuncin da aka yanke masa. Saboda hukuncin da kuma larurar ABS, Ray ya rasa aikinsa.

Amma bai rasa ƙwarin gwiwa ba, ko halinsa na walwala da barkwanci.

"Mutane da dama na tunanin masu ABS na samun yanayin da suke ciki a ɓagas, amma ni dai na fi gamuwa da ɓangaren yawan barci kawai."

People are also reading