Home Back

Kano: 'Yan Sanda Sun Gano Yarinya Mai Shekaru 2 Da Aka Sace a Makota

legit.ng 2024/7/25
  • Rundunar 'yan sandan Kano ta samu nasarar ceto wata yarinya mai suna Amina 'yar shekaru biyu da rabi
  • An ceto ta ne bayan mahaifinta ya shigar da kokensa ga 'yan sanda cewa wani ya kira shi tare da neman kudin fansar N2m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da ceto yarinyar awanni 16 da sace ta cikin koshin lafiya a makota Jihar Kano- Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana nasarar ceto wata yarinya, Amina mai shekaru biyu da rabi daga makocinsu. Tun da fari, mahaifin yarinyar ne ya garzaya ofishin 'yan sanda ya na neman dauki bayan an yi garkuwa da ita.

Yan sanda
An ceto yarinyar da makocinsu ya sace a Kano Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa Asali: Facebook

A sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce an nemi kudin fansa N2m.

An ceto Amina cikin koshin lafiya

Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa ta ceto Amina awanni 16 bayan sace ta a Sabuwar Gandu, Kwarin Barka da ke Kano. Jami'an yaki da garkuwa da mutane ta rundunar ne su ka ceto yarinyar bayan binciken kwa-kwaf. An gano Amina a wani gida bayan makocinsu mai shekaru 22, Zakariyya Muhammad ya sace ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashi Zakariyya ya amsa zargin sata

Matashi mai shekaru 22, Zakariyya Muhammad ya amsa cewa shi kadai ne ya lallaba ya sace Amina, tare da neman mahaifinta ya biya shi kudin fansa.

Matashin ya bayyana cewa Amina 'yar makocinsa ce, kuma da kansa ya yiwa jami'in 'yan sanda jagora har inda ya boye ta a unguwar. Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce likitoci a asibitin kwararru na Murtala sun tabbatar da lafiyar Amina kalau.

SP Kiyawa ya nemi jama'a su rika sa ido kan ayyukan bata gari a yankunansu, tare da mika bayanai ga jami'an 'yan sanda.

An kama 'yan saba 100 a Kano

A baya mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan Kano ta cafke 'yan daba akalla 100 da su ka addabi jama'a cikin kwanaki 10.

Haka kuma an cafke masu garkuwa da mutane guda biyu, 'yan fashi 25 da masu sayar da miyagun kwayoyi ga matasan jihar gida uku.

Asali: Legit.ng

People are also reading