Home Back

RUƊANIN MASARAUTAR KANO: Cif Jojin Najeriya ya yi wa Cif Jojin Kotun Tarayya da na Babban Kotun Kano kiran gaggawa

premiumtimesng.com 2024/7/1
Tsigaggen Sarki Aminu Ado ya shiga Fadar Sarki ta Gidan Nassarawa, yayin da sabon Sarki Muhammadu Sanusi ke cikin Gidan Sarki

Cif Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola ya gayyaci Cif Jojin Babbar Kotun Tarayya da Cif Jojin Babbar Kotun Jihar Kano, dangane da mabambantan hukuncin da suka zartas kan dambarwar shari’ar masarautar Kano.

Mai Shari’a a Babbar Kotun Tarayya ta Kano, S. A A. Amobeda ya bada umarnin ‘yan sanda su fitar da Sarki Muhammadu Sanusi II daga Gidan Sarauta su ɗora tuɓaɓɓen Sarki Aminu Ado.

Yayin da ita kuma Amina Adamu Aliyu ta Babbar Kotun Kano ta bayar da umarnin kada wanda ya sake ta taɓa Sarki Muhammadu Sanusi II ko ƙoƙarin fitar da shi daga Gidan Sarauta.

Yayin da masu sharhi da dama ke ƙorafin cewa Kotun Tarayya ba ta da hurumi wajen shiga lamarin sarautar gargajiya, sai dai kotun jiha, Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya, Yakubu Maikyau ya ce abin da ke faruwa a Kotun Tarayya ta Kano da Babbar Kotun Jihar Kano ya zubar da ƙima da darajar kotuna da shari’a baki ɗaya.

Ya zargi wasu alƙalai da lauyoyi wajen zubar wa kotu daraja.

People are also reading