Home Back

An yi jana’izar 9 daga cikin mutane 15 da wata babbar mota ta ture a Kano

dalafmkano.com 2 days ago

Yanzu haka an yi jana’izar mutane 9 daga cikin kusan 15 da wata babbar mota ta hallaka yayin da Direban motar yake gudun wuce kima, jim kadan da idar da sallar jumu’ar yau, a garin Imawa da ke ƙaramar hukumar Kura a jihar Kano.

A zantawar wakilinmu Mu’azu Musa Ibrahim, da wani daga cikin mazauna yankin, ya ce, Direban babbar motar ya ture mutanen ne bayan da aka idar da sallar juma’a, al’amarin da al’ummar yankin da abin ya shafa suka rufe babbar hanyar ta Kano zuwa Zaria ba shiga babu fita.

Bayan kulle hanyar mutanen sun kafa sharaɗin cewar ba za su buɗe hanyar ba har sai an kammala yin jana’izar dukkanin waɗanda suka rasu.

Mutumin ya kuma ƙara da cewa daga bisani motar ta faɗa cikin wani rami, inda aka nemi direba da yaron motar aka rasa sun gudu.

A cewar sa, “an tabbatar da mutuwar mutane 13, yayin da ya kasance ƴan cikin garin tara baki kuma su huɗu, inda sauran mutanen suka samu raunuka, “in ji shi”

Shima wani shaidar gani da ido ya ce, lokacin da babbar motar tazo wucewa ta wajen ana tsaka da bayar da hannu ne, lamarin da motar ta ture aƙalla mutane 15 da misalin ƙarfe 02:15 na yau Juma’a.

People are also reading