Home Back

Arsenal na son Smith Rowe, Chelsea na son Jhon Duran

bbc.com 2024/7/5

Asalin hoton, Getty Images

.
Bayanan hoto, Emile Smith Rowe

Arsenal na shirin karbar fam miliyan 30 na sayar da dan wasan tsakiya na Ingila Emile Smith Rowe, mai shekara 22. (Football Insider)

Dan wasan Ingila Reiss Nelson, mai shekara 24, ya shaida wa Arsenal ya na son fara gwada sa'ar komawa wata kungiyar. (Athletic - subscription required)

Aston Villa ta bai wa Chelsea damar tattaunawa kan dan wasan gaba na Colombia mai taka mata leda Jhon Duran, mai shekara 20. (Telegraph - subscription required)

Sai dai Blues, ba ta da tabbacin ko za su ci gaba da matsawa kan Duran din. (Guardian),

Villa ma na tuntuba kan dan wasan baya na Netherlands mai bugawa Chelsea tamola Ian Maatsen, 22, wanda ya kwashe kakar wasan da ta wuce a Borussia Dortmund. (Sky Sports)

Everton ta bi sahunTottenham da Aston Villa da kuma West Ham kan son dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Roma Tammy Abraham, mai shekara 26. (Mail)

Manchester United ta shirya tsaf kan dan wasan tsakiya na Ingila mai bugawa Everton tamaula Jarrad Branthwaite, dan shekara 21. (ESPN)

Chelsea ta amince da sharuddan dan wasan Faransa mai taka leda a Crystal Palace Michael Olise, 22, sun kuma shirya biyan makudan kudaden da ya nema domin kammala shirin dauko shi. (Teamtalk)

Manchester City ba za ta amince da sayar da dan wasan gaba na Argentina Julian Alvarez a wannan kakar ba. (Football Insider)

Arsenal na son dan wasan Sifaniya mai taka leda a Athletic Bilbao Nico Williams, kan farashin sama da fam miliyan 42. (Football London)

People are also reading