Home Back

YAƘIN ƘWATAR ‘YANCIN ƘANANAN HUKUMOMI: Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnoni 36 Kotun Ƙoli

premiumtimesng.com 2024/7/3
RAƊAƊIN TSADAR RAYUWA: ‘Kowane gwamna ya karɓi Naira biliyan 30 daga Tarayya, domin raba wa talakawa abinci’ – Sanata Akpabio

Gwamnatin Tarayya ta maka gwamnonin Najeriya 36, inda ta ke roƙon kotu ta tirsasa ƙwatar wa ƙananan hukumomin ƙasar nan 774 cin gashin kan su, wato a riƙa ba su kuɗaɗen su kai-tsaye, ba tare da an bai wa jihohi su ba su ba.

Ofishin Antoni Janar kuma Ministan Harkokin Shari’a na Tarayya ne ya shigar da ƙarar a Kotun Ƙoli, ya na neman kotun ta bai wa ƙananan hukumomin cin gashin kan su.

A cikin ƙara mai lamba SC/CV/343/2024, gwamnatin tarayya na so Kotun Ƙoli ta haramta wa gwamnoni rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi.

Haka kuma ta na so a riƙa tura wa kowace ƙaramar hukuma kuɗaɗen ta kai-tsaye, ba ta hannun gwnonin jiha na.

Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Lateef Fagbemi na kuma so Kotun Ƙoli ta haramta wa gwamnoni naɗa shugabannin riƙon ƙananan hukumomi.

An dai shirya za a saurari ƙarar a ranar 30 ga Mayu.

An daɗe ana ƙorafin yadda gwamnonin jihohi ke sarrafa ƙananan hukumomi.

Ko kwanan nan tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce zaɓen shugabanni ba shi da bambanci da taron naɗa basaraken gargajiya.

People are also reading