Home Back

Daminar Bana: Manoma Su Guji Shuka Da Wuri, Su Rungumi Inshora – Masu Ruwa Da Tsaki

leadership.ng 2024/5/15
Daminar Bana: Manoma Su Guji Shuka Da Wuri, Su Rungumi Inshora – Masu Ruwa Da Tsaki

Masu ruwa da tsaki a fannin aikin noma, sun gargadi manoma a kan su guji yin shuka da wuri a kakar noman bana; ko da kuwa an samu ruwan sama a nan kurkusa.

A cewar tasu, bisa kwarewar da suke da ita a wannan fanni, suna ganin yin shukar da wuri zai iya sanyawa Irin da suka shuka ya yi saurin lalacewa.

Haka zalika, sun shawarce su wajen tabbatar da yin nazari a kan samun sauyin yanayi, kafin fara yin shuka a gonakinsu.

A hirar daban-daban da jaridar LEADERSHIP ta yi da masu ruwa da tsakin sun bayyana cewa, manoman da suke da kwarewa a wannan fanni; ko kadan ka da su dogara a kan saukar ruwan sama na farko da kuma na biyu na wannan shekara, domin ka da Irin da suka shuka ya lalace.

Haka zalika, a nasa bangaren; Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa, Reshen Kudu Maso Yamma (AFAN), Dakta Babafemi Oke, ya shawarci manoman da su sanya gonakinsu a cikin tsarin inshorar aikin noma, wanda hakan zai ba su damar kare amfaninsu da suka shuka daga tafka asarar da za ta iya afkuwa.

Otunba ya ce, ka da manoman su yi gaggawar yin shuka; don takamarsu na ganin saukar ruwan sama na farko da kuma na biyu, inda ya yi nuni da cewa, manoman da ke da kwarewa, ya zama wajibi su yi amfani da ita wajen gyarawa da kuma aiwatar da sharar gonakinsu.

A cewarsa, samun saukar ruwan sama na farko da na biyu, ba shi ne yake nuna samun saukar ruwan sama a kan lokaci ba, musamman duba da illar da za ta iya afkuwa; musamman a sakamakon samun sauyin yanayi.

Ya ci gaba da cewa, koda-yake ruwan saman da ya kamata ya fara sauka a tsakanin watan Afirilu, sai yanzu ya fara sauka a wannan wata da muke ciki na Fabirairu a Arewacin tsakiyar kasar nan. Don haka, akwai bukatar manoma su sanya ido kwarai da gaske kafin su kai ga fara yin shuka.

Har ila yau, ya kuma bukaci manoman da su tabbatar sun sayi Irin noma daga wurin hukumomin aikin noma da aka yi wa rijista, kamar irin su ADP, don gudun ka da su tabka mummunar asara.

Shi ma wani kwararren manomi, Prince Adegbenro Nurudeen cewa ya yi, “Saboda matsalar da ke tattare da samun sauyin yanayi, yana da kyau manoma su yi nazari a kan sauyin yanayi da kuma nau’in Irin da za su shuka, duk kuwa da cewa na san manoma da da dama; wdanda za su kagara su yi shuka musamman ganin cewa, ana samun hauhawar farashin kayan abinci a dukkanin fadin kasar nan”.

Nurudeen ya ci gaba da cewa, “Domin samun yin girbi mai kyau a wannan shekara, dole ne manoma su tabbatar sun yi nazari a kan irin yanayin kasar noma tare da rumgumar dabia’r sauya aiwatar da shuka a gona, duba da yadda yanayin saukar ruwan saman zai kasance”.

Ya kara da cewa, bincike ya nuna; a wasu shiyyoyi na kasar nan, za a iya samun karancin saukar ruwan sama, inda kuma a wasu shiyyoyin, za a iya samun saukar ruwan saman yadda ya kamata.

Binciken da jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa, duk da cewa yin shuka a lokacin damina na da kyau, amma yin hakan a lokacin samun ruwan sama kamar da bakin kwarya, zai iya haifar da samun matsaloi da dama; wadanda suka hada da afkuwar ambaliyar ruwan sama da ka iya janyo asarar amfanin da aka shuka.

People are also reading