Home Back

Gwamnatin Kano ta Sako 'yan Kasuwa a Gaba, Za ta Kori Mutane 5000 Daga Shagunansu

legit.ng 2024/7/4
  • Yan kasuwa kimanin 5000 ne ake fargabar za su rasa shagunansu a jihar Kano bayan hukumar tsara birane ta KNUPDA ta umarce su da gaggauta tashi cikin awanni 48
  • Rahotanni sun tabbatar da hukumar ta umarci masu shaguna da ke filin masallacin idi har zuwa titin IBB way da su gaggauta kwashe kayansu ko su fuskanci fushin hukuma
  • Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Yakubu Muhammad ya ce sun shafe shekaru 18 a shagunan da masarautar Kano da tsohuwar gwamnati ta mallakawa matasa domin ba su aikin yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Akalla ‘yan kasuwa 5000 ne za su rasa shagunansu da ke masallacin filin idi da ke jihar Kano bayan hukumar tsara birane ta KNUPDA ta umarce su da su tashi.

Hukumar KNUPDA ta ba masu shaguna a masallacin filin idi da ke hanyar IBB way awanni 48 su kwashe kayansu tare da barin wurin ko su fuskanci fushin hukuma.

Abba Kabir
Gwamnati ta kori 'yan kasuwa 5000 daga shagunansu Hoto: Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

Punch News ta wallafa cewa masu shagunan sun bayyana cewa wannan umarni ya jefa su cikin tashin hankali, domin ba su san inda za su nufa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekararmu 18 a shagunanmu,’ Yan kasuwa

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Yakubu Muhammad ya bayyana cewa shekararsu 18 a shagunan da gwamnatin Kano da masarauta ta ba su.

Ya ce tsohon galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim ne ya shige gaba domin rage zaman banza tsakanin matasa masu kwacen waya da sauran ayyukan bata-gari.

Yakubu Muhammad ya yi zargin raba matasan da shagunasu zai janyo barazanar tsaro ga jihar Kano, kamar yadda Voice of Nigeria ta wallafa.

'Yan kasuwa sun roki gwamna Kano

‘Yan kasuwar da hukumar KNUPDA ta ba izinin tashi daga shagunansu sun roki gwamna Abba Kabir Yusuf ya shiga batun.

Sun ce su na daga wadanda su ka jajirce wajen zabar gwamnan, saboda haka su na fatan ba zai zura idanu a kore su daga shagunansu ba.

Gobara ta tashi a Kano

A wani rahoton kun ji cewa wata gobara ta tashi a kwalejin fasaha ta Kano, inda ta kone sashen Arts and Industrial na kwalejin wanda ya jawo dimbin asara a safiyar ranar Talata.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara ta Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce har yanzu ba a san dalilin afkuwar ta ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading