Home Back

"Ban San Aminu Ado Ba": Kwamishinan ’Yan Sanda Ya Fadi Matsayarsa Kan Rigimar Kano

legit.ng 2024/7/6
  • Kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, Salman Garba ya magantu kan yadda zai yi aiki a jihar duk da rigimar sarauta
  • Sabon kwamishinan ya bayyana cewa ya zo Kano ne domin yin aiki ba kare muradun wasu tsiraru ba a jihar
  • Garba ya kuma yi fatali da labarin cewa yana da alaka da Aminu Ado Bayero inda ya ce a yau ya fara jin labarin shi ma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, Salman Garba ya yi martani kan rigimar sarautar jihar.

Garba ya ce ya zo Kano ne domin aiki ga 'yan kasa da kuma Najeriya ba kare muradun wasu ba.

Sabon kwamishinan ya bayyana haka ne yayin da ya ke amsa tambayoyi kan yadda zai dakile rigamar sarautar jihar, cewar The Nation.

Rahorannin sun yi nuni da cewa Garba yana da alaka da Aminu Ado Bayero yayin da ya fito daga jihar Kwara inda mahaifyar tsohon sarkin ta fito.

Sai dai kwamishinan yayin hirar ya ce shi ma a yanzu ya fara jin wannan labari da ake yadawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ya zo Kano ne domin yin aiki ba tare da nuna wariya na addini ko wani kabilanci ba.

"Farko dai ni dan Najeirya ne kuma na zo ne domin bautawa 'yan kasar, labarin Bayero yana da alaka da ni yanzu na fara ji nima.
"Ni dai na zo Kano ne domin bautar jama'a kuma zan yi duka mai yiwuwa domin tabbatar da dakile matsalolin jihar."

- Salman Garba

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading