Home Back

Biden da Trump sun yi luguden laɓɓa yayin muhawara

bbc.com 5 days ago
.

Asalin hoton, CNN

Shugaban Amurka Joe Biden na jam'iyyar Democrat ya kara da abokin hamayyarsa na Republican, tsohon shugaban kasar Donald Trump, a wata muhawara da gidan talabijin na CNN ya gudanar.

An shafe awa daya da rabi ana tattauna batutuwa da dama da suka shafi kasar da siyasar duniya, kuma miliyoyin mutane daga ciki da wajen Amurka sun kashe kwarkwatar idanunsu.

A yayin mahawara tsohon shugaban kasarDonald Trump ya zillewa tambayar da aka yi masa kan hannu a karya dokar da wasu magoya bayansa suka yi ranar 6 ga watan Janairun 2021 lokacin da majalisun dokokin kasar ke tattara bayanan nasarar Biden.

A yayin mahawara yan takarar shugaban ƙasar Amurka, da aka tambayi Donald Trump ko zai amince da bukatun Putin wajen kawo ƙarshen yaƙin da yake da Ukraine da suka hada da barwa Rasha yankunan Ukraine da Rashar ta kwace ?, sai ya ce hakan ba abu ne mai yiwuwa ba.

"Zan tabbatar na daidaitaPutin da Zalensikey, kafin na karɓi rantsuwa a ranar 20 ga watan Janairun mai zuwa, zan kawo ƙarshen wannan yaƙi da ake yi, ana kashe mutane ba ƙaƙautawa, kuma zan samar da daidaito cikin hanzari kafin ma na shiga ofishin shugaban ƙasa" a cewar Trump.

Shugaban ƙasar Joe Biden ya bayyana Trumph a mastayin wanda kotu ta kama da babban laifi:

"Mutumin da ke tsaye da ni a nan mai laifi ne, kotu ta same shi da aikata babban laifi, kuma abin da ya ke faɗa a nan ko kaɗan babu gaskiya a cikinsa''

Sai dai Trump ya mayar masa martani da cewa ai shima dansa Hunter Biden kotu ta kama shi da laifin mallakar bindiga ba bisa ka'ida ba.

Mutanen biyu dai sun yi ta musayar bakaƙen maganganu a tsakaninsu, inda suke zargin juna da rashin katabus a mulkinsu.

Batutuwan da suka fi jan hankali a muhawarar sune baƙin haure, kiwon lafiya, zubar da ciki da kuma yaƙe yaƙen da ake fama da su a duniya.

People are also reading