Home Back

Tsoho Mai Shekara 70 Ya Shiga Hannu Kan Safarar Wiwi

leadership.ng 2024/7/6
Tsoho Mai Shekara 70 Ya Shiga Hannu Kan Safarar Wiwi

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA, sun kama wani tsoho mai shekara 70 dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 57.2 a Jihar Nasarawa tare da kwace hodar Iblis da kudinta ya kai sama da Naira biliyan 2.1. 

An kama wannan wannan nau’in tabar wiwi na roba a tashar ruwa ta Fatakwal, da kuma filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

Kazalika jami’an dai sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da safarar tabar wiwi mai nauyin kilogiram 426 a Jihar Ekiti.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Hukumar NDLEA, Femi Babafemi.

Kazali Hukumar ta kaddamar wasu kame a Babban Birnin Tarayya Abuja da Katsina da kuma Jihar Nasarawa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Jami’an ‘yansandan sun kama wasu manya-manyan kayayyakin tabar wiwi da kudinsu ya haura Naira 2.1 a kan tituna a tashar jiragen ruwa na Fatakwal, Onne da filin jirgin Murtala Muhammed da ke Ikeja.

“A filin jirgin saman Legas, jami’an tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro a ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu, 2024, sun kama wani babban kaya a cikin akwatuna guda takwas, dauke da fakiti 320 da nauyin kilogiram 164.50 na kayayyaki masu nauyi daga Kanada a kan jirgin sama samfurin KLM na Kasar Amsterdam, Netherlands.

“Kayyakin da aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan 960 wanda wani fasinja, Ughenu Nnaife Francis ya shigo da shi. Jami’an hukumar NDLEA, kwastam da sauran su ne suka gano shi a dakin karbar fasinjoji na E-ishort na filin jirgin sama a yayin wani aikin karbar fasinjoji na hadin gwiwa da jami’an tsaro suka gudanar a yayin da jami’an suka gudanar da bincike a kai, lokacin da wanda ake zargin ke yunkurin fitar da akwatunan daga zauren.”

A cewar sanarwar, wanda ake zargin da aka kama a filin jirgin sama na Legas ya yi ikirarin cewa an dauke shi aikin safarar kwayoyin ne daga Kasar Kanada zuwa Nijeriya a kan kudi Naira miliyan 6.

Ya ce shi dan Kasar Jamus ne amma ya je Toronto ne domin karbar magungunan, sannan an kama shi da wani kaso mai yawa na Loud, wani nau’in tabar wiwi wanda kudinsa ya kai Naira miliyan 960.

A halin da ake ciki kuma, jami’an NDLEA da ke harabar tashar jiragen ruwa ta Fatakwal sun kama wata kwantena da ta taso daga Kasar Indiya dauke da katan 1,750 na hodar Iblis mai nauyin kilogiram 26,250 kuma darajarsa ta kai Naira biliyan 1.225. Kwantenar mai lamba TEMU 6807401, an nufi Enugu da ita ne, kuma an gano ta lokacin wani aiki na hadin gwiwa da hukumar NDLEA, da kwastam, da sauran hukumomin tsaro suka gudanar.

‘Yansandan sun kuma kama wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Blessing Thomas a Abuja a ranar 31 ga watan Mayu bayan da aka samu kilo 1 na sinadarin methamphetamine a hannunta, tana tafiya ne a cikin motar bas daga Legas zuwa Yola, Jihar Adamawa, an kama ta a kan hanyar Kwali zuwa Gwagwalada.

Sanarwar ta kara da cewa, “Haka zalika jami’an tsaro a Jihar Nasarawa sun kama wani tsoho mai suna Muhammadu Ibrahim dan shekaru 70 da haihuwa da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 57.2 a garin LafiYa babban birnin jihar.

“An kama mutum biyu Suleiman Kazeem mai shekaru 35 da Sunday Gbenga mai shekaru 20 a lokacin da jami’an NDLEA suka kai farmaki dajin Ara, Ara-Ekiti a Jihar Ekiti inda suka kwato kilogiram 426 na tabar wiwi da tuni aka shirya su a cikin manyan buhuna, da sama da kilogiram 4,000 na sinadari iri daya da ya kai noman sama da kadada 1.66.

“A Jihar Katsina kuwa, an kama wani dan Nijar mai suna Suleman Audu, mai shekaru 29, 76 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 42, a bayan da jami’an NDLEA suka kama shi a hanyar Zaria zuwa Malumfashi.”

People are also reading