Home Back

Jami’ar Maryam Abacha za ta horas da ma’aikatan Muryar Najeriya VON kyauta

premiumtimesng.com 2024/4/28
Jami’ar Maryam Abacha za ta horas da ma’aikatan Muryar Najeriya VON kyauta

Darakta Janar na Muryar Najeriya (VON), Jibrin Baba Ndace, ya bayyana shirin gidan rediyon na yin hadin gwiwa da Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) da nufin faɗaɗa manufar wannan jami’a ga kasashen duniya.

Ndace ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya kai wa shugaban jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ziyara a yammacin ranar Juma’a a Kano.

Ya ce tashar a shirye ta ke ta hada kai da mahukuntan jami’ar domin tallata sabuwar jami’ar ba a Najeriya kadai ba har ma da kasashen waje.

“A shirye nake in kasance a sahun gaba wajen tallata jami’ar, ba a Najeriya ba kadai ba har ma ga sauran kasashen duniya. Akwai labarai masu kyau da ke faruwa a Najeriya kuma daya daga cikinsu ita ce wannan jami’a.

“Muna da mutanen da suke yi wa kasarmu aiki tukuru don ci gabanta da kuma don ta bunƙasa ta fannoni da dama kuma Farfesa Gwarzo na kan gaba wajen haka. Daga yau labarin MAAUN zai kasance daya daga cikin abubuwan da VON ta sa gaba,” in ji Ndace.

Shugaban rukunin jami’o’in Maryam Abacha Farfesa Adamu Gwarzo, a jawabinsa ya bayyana cewa jami’sr za ta baiwa ma’aikatan VON ɗin horo ma musamman kan yadda za du riƙa gudanar da ayyukan su, musamman a fannin yaɗa labarai da sauransu.

” Za mu tallafa muku matuƙa wajen ba ma’aikatanku horo. Kuma za mu yi haka ne kyauta ba tare da kun biya ba