Home Back

'Gina Legas': Sule Lamido Ya Ragargaji Tinubu, Ya Fadi Yadda PDP Za Ta Ceto Najeriya

legit.ng 2024/6/29
  • Jigo a jam'iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana yadda Bola Tinubu ya gaza tabuka komai a Najeriya
  • Sule Lamido ya bayyana gaskiya kan maganar da ake cewa Bola Tinubu ne ya gina jihar Legas a lokacin da yake gwamnan jihar
  • Har ila yau Lamido ya fadi irin matakin da jam'iyyar PDP take dauka domin ceto al'ummar Najeriya daga mulkin jam'iyyar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jami'yyar adawa ta PDP, Sule Lamido ya caccaki salon mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sule Lamido ya ce lallai akwai kurakurai a tsarin jam'iyyar APC wanda hakan ne ya kai Najeriya halin da take ciki na matsin rayuwa.

Sule Lamido
Sule Lamido ya ce Tinubu bai gina Legas ba. Hoto: Sule Lamido Asali: Facebook

Tsohon gwamnan ya yi jawabin ne a wata hira ta musamman da ya yi a gidan talabijin din Channels a jiya Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta lalata Najeriya

Sule Lamido ya bayyana cewa komai bai tafiya daidai a Najeriya saboda irin kama karya da APC take yi a kasar, rahoton Daily Trust.

Ya kara da cewa tun zuwan APC a 2015 ba su da manufa sai dai kawai su ci zabe. Kuma haka abin yake tafiya har a mulkin Bola Tinubu.

Tinubu ya gina Legas?

A cikin hirar, Sule Lamido ya ce an yaudari mutane da cewa Tinubu ya gina jihar Legas amma a gaskiya ba haka lamarin yake.

Lamido ya ce an gina Legas ne da kudin gwamnatin tarayya musamman wajen samar da haraji a tashoshin jiragen ruwa da na sama.

PDP na shirin ceto Najeriya

Kamar yadda Sule Lamido ya bayyana, a yanzu haka jam'iyyar PDP na kan hanyar dunkulewa waje guda domin samar da mafita ga Najeriya.

Sule Lamido ya ce yan Najeriya sun ji a jika kuma suna kiran PDP da ta kawo musu agaji saboda haka jam'iyyar tana kan shirye-shiryen kawar da APC a 2027.

Jigon APC ya koka da mulkin Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC, Lukman Salihu ya koka kan yadda shugaba Bola Tinubu ke jagorantar Najeriya.

Lukman Salihu ya ce jam'iyyar APC ta dauki hanyar lalacewa saboda a yanzu haka duk abin da aka zargi PDP da shi a baya APC na aikata shi.

Asali: Legit.ng

People are also reading