'Gina Legas': Sule Lamido Ya Ragargaji Tinubu, Ya Fadi Yadda PDP Za Ta Ceto Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jami'yyar adawa ta PDP, Sule Lamido ya caccaki salon mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sule Lamido ya ce lallai akwai kurakurai a tsarin jam'iyyar APC wanda hakan ne ya kai Najeriya halin da take ciki na matsin rayuwa.
Tsohon gwamnan ya yi jawabin ne a wata hira ta musamman da ya yi a gidan talabijin din Channels a jiya Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sule Lamido ya bayyana cewa komai bai tafiya daidai a Najeriya saboda irin kama karya da APC take yi a kasar, rahoton Daily Trust.
Ya kara da cewa tun zuwan APC a 2015 ba su da manufa sai dai kawai su ci zabe. Kuma haka abin yake tafiya har a mulkin Bola Tinubu.
A cikin hirar, Sule Lamido ya ce an yaudari mutane da cewa Tinubu ya gina jihar Legas amma a gaskiya ba haka lamarin yake.
Lamido ya ce an gina Legas ne da kudin gwamnatin tarayya musamman wajen samar da haraji a tashoshin jiragen ruwa da na sama.
Kamar yadda Sule Lamido ya bayyana, a yanzu haka jam'iyyar PDP na kan hanyar dunkulewa waje guda domin samar da mafita ga Najeriya.
Sule Lamido ya ce yan Najeriya sun ji a jika kuma suna kiran PDP da ta kawo musu agaji saboda haka jam'iyyar tana kan shirye-shiryen kawar da APC a 2027.
A wani rahoton, kun ji cewa, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC, Lukman Salihu ya koka kan yadda shugaba Bola Tinubu ke jagorantar Najeriya.
Lukman Salihu ya ce jam'iyyar APC ta dauki hanyar lalacewa saboda a yanzu haka duk abin da aka zargi PDP da shi a baya APC na aikata shi.
Asali: Legit.ng