Home Back

Gobarar Dare Ta Kone Shaguna 40 A Kano

leadership.ng 2024/5/3
Gobarar Dare Ta Kone Shaguna 40 A Kano

Akalla shaguna 40 ne suka kone a wata gobara da ta barke a daren ranar Talata a karamar hukumar Kumbotso da ke jihar Kano.

Shaguna 40 da abin ya shafa na cikin wani katafaren rukunin kasuwanci ne a cikin birnin Kano.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, kimanin shaguna 40 ne a harabar kasuwancin da ke makwabtaka da jerin gidaje na Zawaciki ne gobarar ta kone kurmus.

Wani ganau mai suna Musa Ahmad ya shaida wa manema labarai cewa, shagunan da abin ya shafa sun hada da shagunan sayar da kayayyakin masarufi, shagunan siminti, shagunan PoS, da dai sauransu.

Sai da hukumar kashe gobara ta jihar ta yi amfani da motar ruwa Uku kafin a samu a kashe gobarar.

People are also reading