Home Back

Eid El Kabir: An Sace Ragon Layya Na Babban Malamin Arewa a Daren Ranar Sallah

legit.ng 2024/7/2
  • Wasu ɓata gari sun sace ragon layya na babban Limamin kauyen Mista Ali a ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato
  • Limamin da ya ja Sallar idi a garin, Malam Haruna Yakub ne ya bayyana haka a cikin huɗubarss bayan sallame Sallah raka'a biyu ranar Lahadi
  • Malam Haruna ya nuna damuwarsa da mamakin yadda mutane suka lalace, inda ya yi tunatar da cewa za a yi kowa hisabi ranar lahira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Wasu ɓarayi sun sace ragon layya na babban limamin Masallacin garin Mista Ali a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Ɓata garin sun ɗauke ragon ne yayin da ake tsaka da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a daren ranar Babbar Sallah a gidan limamin.

Satar ragon layya a Jos.
Barayi sun ɗauke ragon layyar babban limami a Jos Hoto: Nur Photo Asali: Twitter

Malam Haruna Yaqub, wani malamin Addinin Musulunci ne ya bayyana haka a cikin huɗubar da ya yi bayan kammala raka'o'i biyu na Sallar Idi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Limamin ya yi Alla-wadai da sace ragon layyar babban Malaminsu, yana kai bayyana lamarin da muguwa ɗabi'a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

"Jiya daddare aka sace ragon da babban Limaminmu ya sayo domin ya yi layya, lamarin da tada mana hankali, mun yi mamakin sace ragon Liman.
"Wannan na nufin mutane ba su jin tsoron Allah, yanzu mun mun yi lalacewar da mutane za su sace ragon da aka saya domin yin ibadar addini," in ji Malam Yakub.

Malam Haruna ya kuma yi kira ga jama’a da su ji tsoron Allah, su daina sata ko saikata wasu miyagun laifuka.

Ya kuma jan hankalin mutane da tunatar da su cewa Allah SWT zai yi kowa hidabin ayyukansa a ranar gobe ƙiyama.

"Wannan shi ne lokacin da ya dace mutane su tubar ma Allah su koma kan tafarki madaidaici, ya kamata mutane sun daina saɓawa Allah, su maida hankali wajen yin ayyukan alheri."

Matasa sun tada hargitsi kan naɗin sarauta

A wani rahoton kuma matasa sun ɗauki zafi, sun farmaki jami'an gwamnati, ƴan sanda da sojoji a wurin bikin naɗin Sarkin Nkomoro a yankin Ezza ta Arewa a Ebonyi

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne daga lokacin da wakilin gwamnati ya faɗi sunan wanda za a naɗa a matsayin sabon sarki.

Asali: Legit.ng

People are also reading