Home Back

Kasar Sin Na Maraba Da Abokai ‘Yan Kasuwa Daga Kasashe Daban Daban Da Su Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar

leadership.ng 2024/5/2
Kasar Sin Na Maraba Da Abokai ‘Yan Kasuwa Daga Kasashe Daban Daban Da Su Ci Gaba Da Zuba Jari A Kasar 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya ce, kasarsa na maraba da abokai ‘yan kasuwa daga kasashe daban daban da su ci gaba da zuba jari da ma zurfafa kasuwanci a kasar.

Jami’in ya yi tsokacin ne a yayin da yake amsa tambayoyi game da taron shekara shekara na dandalin tattaunawa kan ci gaban kasar Sin na 2024 a gun taron manema labaru da aka saba yi na yau Litinin ranar 25 ga wata.

Kakakin ya kuma kara da bayyana cewa, ba tare da la’akari da sauyin yanayin kasa da kasa ba, kasar Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa da mu’amala da kasashen duniya, tare da samar da sabbin damammaki ga duniya daga sabbin ci gaban da take samu.

Game da tsokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi game da yankin Hong Kong na kasar Sin, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin tana bayyana rashin gamsuwa da kakkausar murya ga yadda Amurka ke ci gaba da yin katsalandan da bata sunanta dangane da dokokin kiyayen tsaron kasa na Hong Kong, tare kuma da kalubalantar Amurka da ta gaggauta daina tsoma baki cikin harkokin Hong Kong, da ma na cikin gidan kasar Sin.

Haka zalika, yayin da yake amsa tambaya game da gazawar kwamitin sulhu na MDD wajen amincewa da daftarin kudurin tsagaita bude wuta a zirin Gaza da Amurka ta gabatar, Lin Jian ya ce, akwai bukatar kwamitin sulhun ya inganta tsagaita bude wuta mai dorewa ba tare da wani sharadi ba, yana mai cewa wannan kira ne na duniya baki daya.

Ya ce ya kamata duk wani mataki da kwamitin sulhun zai dauka ya zama mai dorewa kuma bisa sanin ya kamata. Haka kuma, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kwamitin sulhun wajen kara daukar matakai masu ma’ana. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

People are also reading