Home Back

Sheikh Musa Lukwa ya gudanar da sallar Idi ranar Talata a Sokoto, ya ce ya bi Nijar tunda sun ga wata

premiumtimesng.com 2024/5/10
Sheikh Musa Lukwa ya gudanar da sallar Idi ranar Talata a Sokoto, ya ce ya bi Nijar tunda sun ga wata

Duk da sanarwar rashin ganin wata a Najeriya da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya yi ranar Litinin, da ya sa aka cika azumi 30 a Najeriya, Shehin Malami, Musa Lukwa dake Sokoto ya gudanar da Sallar Idi a cikin Masallacin sa dake Sokoto.

Sheikh Lukwa ya ce an ga wata a kasar Nijar wanda hakan ya sa shima zai gudanar da sallar Idi a ranar Talata.

Mun samu tabbacin ganin wata a kasar Nijar, saboda haka mun yi sallar Eid yau Talata a garin Sokoto.

“Ba wai ina cewa dukkan Musulmin Najeriya dole ne su yi Sallar Idi a ranar Talata ba, amma ba mu da wata hujjar rashin yin Sallarmu a ranar Talata, domin makwabtanmu sun ga sabon wata. Kuma ku tuna, babu azumi ranar Sallah. haramun ne.”

Lukwa ya bayyana cewa sarkin Musulmi na tilasta wa musulman Najeriya su bi kasar Saudiyya, wanda hakan ya saba wa karantar war Annabi SAW. Sannan kuma ya Kalubalanci duk wani malami da ya musanta shi ya zo su buga mukabala akai.

“Idan za mu iya yarda da na Saudiyya, me ya sa ba za mu yarda da na Jamhuriyar Nijar ba, wanda ke kusa da mu.

Sai dai kuma rahotanni sun nuna cewa

People are also reading