Home Back

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Fitaccen Sarki Mai Daraja Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Landan

legit.ng 2024/7/1
  • Fitaccen basarake a jihar Ogun, Oba Olufemi Ogunleye ya mutu a wani asibiti a Landan ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, 2024
  • Rahotanni sun nuna cewa Sarkin ya rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya yana da shekara 79 a duniya
  • Marigayi sarkin ya kasance tsohon ɗan jarida wanda ya yi aiki da tsohuwar jaridar Daily Times kuma ya yi ritaya daga aikin gwamnati

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Sarkin Akinale wanda ake kira da Towulade na Akinale a ƙaramar hukumar Ewekoro da ke jihar Ogun, Oba Olufemi Ogunleye ya riga mu gidan gaskiya.

Fitaccen basaraken mai daraja ya rasu ne yana da shekaru 79 a duniya ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, 2024.

Oba Olufemi Ogunleye
Allah ya yi wa wani sarki a jihar Ogun, Oba Olufemi Ogunleye rasuwa Hoto: Aba Hafa Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Sarkin ya sha fama da rashin lafiya a wasu lokuta daban-daban kuma ana kai shi asibitin St. Thomas da ke Landan a ƙasar Ingila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a wannan karon Allah ya karɓi rayuwarsa da yammacin ranar Laraba a asibitin Landan, Punch ta ruwaito.

Wata majiya da ke da kusanci da marigayi Sarkin, ta shaida wa manema labarai cewa marigayin bai jima da kammala karatunsa na digiri na uku a fannin shari’a ba.

"Towulade na Akinale, Oba Olufemi Adewunmi Ogunleye ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 79 a duniya a wani asibitin Landan bayan gajeruwar rashin lafiya."
"Muna addu'ra ruhinsa ya samu salama a wurin Ubangiji, Amin."

Takaitaccen tarihin Oba Ogunleye

Marigayi Oba Ya Ogunleye kasance babban dan jarida wanda ya yi aiki da tsohuwar fitacciyar jaridar nan Daily Times ta Najeriya.

Ya yi ritaya daga aiko a lokacin yana matsayin manajan sashin hulda da jama'a na kamfanin sufurin jiragen sama na Najeriya watau Nigeria Airways wanda aka rushe.

Tsohon Gwamna Gbenga Daniel ne ya fara nada shi a matsayin Baale na Akinale a shekarar 2004 kuma yana cikin wadanda wannan gwamnatin ta ɗaga darajarsu zuwa Oba a 2006.

Alhazan Masar 60 sun rasu a Saudiyya

A wani rahoton kuma ƴan uwa da abokan arziki na ci gaba da laluben Alhazan ƙasar Masar da suka ɓata ranar Laraba, 19 ga watan Yuni, 2024.

Bayanai sun nuna cewa akalla alhazai 600 da suka fito daga Masar ne suka riga mu gidan gaskiya a ƙasa mai tsarki a lokacin aikin Hajjin bana.

Asali: Legit.ng

People are also reading