Home Back

Ƙungiyar Ɗalibai Ta Yi Barazanar Zanga-zanga Saboda Ƙarancin Man Fetur

leadership.ng 2024/5/18
Ƙungiyar Ɗalibai Ta Yi Barazanar Zanga-zanga Saboda Ƙarancin Man Fetur

Kungiyar daliban Nijeriya ta kasa, NANS ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga matukar gwamnatin tarayya ta gaza daukar matakin gaggawa na magance matsalar karancin man fetur a kasar.

Shugaban kungiyar, Babatunde Akinteye, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya koka da cewa, karancin man fetur ya jefa ‘yan kasar da dama ciki har da dalibai cikin takaici da damuwa.

NANS ta kuma bukaci Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin Mai na NNPCL, Mele Kyari, da ya yi murabus idan har ba zai iya daukar kwararan matakan magance matsalar karancin man fetur ba.

LEADERSHIP ta rahoto cewa, dogayen layuka sun sake kunno kai a gidajen mai a fadin kasar nan tun a makon da ya gabata kuma har yau lamarin kara ta’azzara yake yi duk da tabbacin da kamfanin na NNPC ya yi na cewa, an shawo kan matsalolin kayan aikin da suke haddasa irin wannan kalubale.

Wakilanmu sun ruwaito cewa, baya ga gidajen mai na NNPC da ke sayar da mai akan farashin Naira 617 a kowace lita, gidajen mai masu zaman kansu a Abuja, babban birnin kasar na sayarwa daga N690, N700 zuwa N800. A daya bangaren kuma, ’yan kasuwar bunburutu na sayarwa daga Naira 1,000 zuwa Naira 1,500 ga kowace lita.

People are also reading