Home Back

‘Kwankwaso da Ganduje’: Hanya 1 da Za a Bi a Samu Zaman Lafiya a Kano Inji Jigon APC

legit.ng 2024/6/28
  • An cigaba da nuna damuwa a kan rikicin siyasa da ke tsakanin shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Rabi'u Kwankwaso
  • Wani jigo a jam'iyyar APC, Alhassan Yaryasa ya yi kira na musamman ga Ganduje da Kwankwaso domin kawo karshen rikicin su
  • Alhassan Yaryasa ya ce babu yadda za samu zaman lafiya a Kano matukar mutanen biyu sun cigaba da zaman doya da manja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Wani jigo a jam'iyyar APC, Alhaji Alhassan Yaryasa ya koka kan yadda rikicin Ganduje da Kwankwaso ya ki karewa.

Alhaji Alhassan Yaryasa ya ce akwai bukatar sasanta rikicin siyasa da ke tsakanin shugaban APC, Abdullahi Ganduje da Sanata Rabi'u Kwankwaso.

Kwankwaso
An bukaci sulhu tsakanin Ganduje da Kwankwaso domin samar da zaman lafiya. Hoto: Abullahi Umar Ganduje|Rabi'u Musa Kwankwaso Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Alhassan Yaryasa ya ce a yanzu Kano na bukatar zaman lafiya wanda zai yi wuyar samu matukar jagororin suna fada da juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje vs Kwankwaso: A yiwa juna gafara

Alhaji Alhassan Yaryasa ya ce akwai bukatar Abdullahi Ganduje da Rabi'u Kwankwaso su yiwa juna gafara domin wanzar da zaman lafiya a Kano.

Ya ce wannan ita ce kawai hanyar da za a bi wajen ganin an samu sulhu a tsakaninsu kuma a samu zaman lafiya da cigaba a jihar Kano.

Yaryasa: "Kirana ga al'ummar jihar Kano"

Har ila yau Alhaji Alhassan Yaryasa ya kira mutanen Kano da su cigaba da hadin kai da zaman lafiya a tsakaninsu ba tare da nuna bambanci siyasa ba.

'Dan siyasar ya ce hakan ne kawai zai kawo masu cigaba a jihar kasancewar ba wani nau'i na cigaba da zai samu sai da zaman lafiya.

Magana kan rusa masarautun Kano

Alhaji Alhassan Yaryasa ya yi martani kan abin da ya shafi rusa masarautun jihar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

Ya ce lallai akwai cin fuska a siyasance ga tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje wajen rusa masarautun.

Alhaji Yaryasa ya kara da cewa ba lallai rusa masarautun ya kawo wani nau'in cigaba a jihar Kano ba.

Ganduje ya yi magana kan Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa Dakta Abdullahi Ganduje ya yi magana kan masu tunanin alaƙarsa da Kwankwaso ba zat ayi ƙarko ba ko sun haɗu a APC.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya ce yana da ƙwarin guiwar za su sake haɗewa wuri ɗaya domin tun asali a tare aka gansu.

Asali: Legit.ng

People are also reading