Home Back

Yadda ake yaƙi da kaciyar mata ta hanyar tiyata: 'Ƴanzu na zama cikakkiyar mace'

bbc.com 2024/8/21

Asalin hoton, Shamsa Sharaawe

Shamsa Sharaawe laying in a hospital bed after the reconstruction surgery.
Bayanan hoto, Shamsa Sharaawe tana murmurewa a asibiti bayan an yi ma ta tiyata
  • Marubuci, Bushra Mohamed
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Aiko rahoto daga London

Gargadi: Wannan labari na dauke da bayanan da ke iya tayar da hankalin mai karatu.

''Hankalina ya yi matuƙar tashi kan batun a sake yanka ni, duk da cewa dai da son raina ne. Amma ya zame min dole in yi hakan saboda lafiyar jikina.''

Shamsa Sharaawe take bayani kan shawarar da ta yanke ta yin tiyatar gyaran jiki bayan da aka yi mata kaciya shekara 25 da suka gabata, a lokacin da take da shekara shida kacal da haihuwa.

An yi mata wannan kaciya (FGM) ne a Somaliya da haɗin bakin danginta kuma wata ungozomar gargajiya ce ta yi mata aikin a gida.

Sama da mata miliyan 230 a duniya ne aka yi wa kaciya, a cewar wani rahoton hukumar UNICEF na baya bayan nan.

A Somaliya da Guinea da Djibouti, akan yi wa yawancin ƴan mata kaciya a kusan kashi 90 cikin dari na al'ummar ƙasashen.

A waɗannan ƙasashe an yi amanna cewa kaciyar tana tabbatar da budurcin yarinya - wani abin da ake alfahari da shi a waɗannan al'ummomin.

Da yawa daga cikin al'ummar Somaliya sun yi amanna cewa budurcin mace abu ne da ke nuni da kimar danginta.

Suna da yaƙinin cewa mutuncin dangi zai ci gaba da wanzuwa idan har aka yi wa budurwa kaciya.

Yawancin al'ummar Somaliya na ɗaukar matan da ba a yi wa kaciya ba, a matsayin waɗanda ba su da ɗabi'a ta kwarai kuma masu sha'awa mai ƙarfi, kuma suna ganin cewa hakan na iya lalata mutunci da kimar dangi gaba ɗaya.

Asalin hoton, Dr Adan Abdullahi

Dr Adan performing surgery at his clinic in Nairobi
Bayanan hoto, Dr Adan yana aikin tiyata a asibitinsa da ke Nairobi

Yayin da ta ke tasowa Shamsa ta ce takan fuskanci azabar ciwo a duk lokacin da ta yi al'ada.

Ta ce: “Kawai ba na son in sake jin irin wannan zafin.'' A cewarta.

A ƙarshen 2023, lokacin da take da shekaru 30, Shamsa ta yanke shawarar duba yiwuwar sake yi mata aiki don kawo ƙarshen azabar zafin da ta ke ji.

A wannan lokacin tana zaune a Burtaniya kuma ta zama mai fafutukar kare haƙƙin jama'a a shafukan sada zumunta da ke yaƙi da kaciyar matan.

Sanin cewa mata da yawa da ke cikin irin halin da take ciki ba su san ko za su iya yin wani abu don inganta rayuwarsu ba ya sa ta yanke shawarar wayar da kan jama'a game da tiyata.

''Babu isassun bayanai game da tiyatar kanta. Wannan shi ne dalilin da ya sa nake magana a kan lamarin,'' in ji Shamsa.

Ana yin aikin tiyatar ne don inganta rayuwa, ba don ado ba. Ya ƙunshi sake gyara inda aka yanke a lokacin kaciyar domin a rage ciwo da kuma inganta rayuwar mace.

A wasu lokuta akan sake faɗaɗa farjin mace domin ya koma yadda yake a baya.

Bayan zurfafa bincike, Shamsa ta gano cewa a Jamus ne zaɓin da take da shi na samun tiyata.

Ta kafa shafin tattara kuɗaɗe ta hanyar dandalin bayar da tallafi na jama'a kuma ta yi nasarar tara dalar Amurka dubu 31.

Amma, duk da yunƙurin da magoya bayanta suka yi, waɗanda wasunsu ba su taɓa jin labarin kaciyar mata ba, ta gano cewa ba ta da isassun kuɗaɗen da za ta iya biyan kuɗin tiyatar.

A karshe Shamsa ta kashe sama da dalar Amurka 37,000 (£30,000) wajen tabbatar da kula ga ƴarta da ta tashi zuwa Jamus da kuma yi mata aikin.

Wannan ya sanya ta fada cikin ƙangin bashi kuma har yanzu asibitin na bin ta Yuro 3800.

"Ban iya komawa domin samun kulawar bayan tiyata ba, saboda abin takaicin shi ne ba zan iya biya ba," in ji Shamsa wadda har yanzu ba ta ga likita ba tun bayan tiyatar da aka yi mata.

"Gaskiya akwai rashin adalci idan aka sanya ka kashe maƙudan kuɗaɗe kan abin da ba kai ka ɗora wa kan ka ba."

Asalin hoton, Dr Reham Awwad

Dr Reham Awwad in the center. She's doing a surgery at her clinic in Egypt.
Bayanan hoto, Dokta Reham Awwad a asibitinta da ke Masar ba ta yarda cewa tiyata ita ce mafi kyawun zaɓi ga duk matan da aka yi wa kaciya ba

Tiyata magani ce?

Akwai nau'ukan kaciyar mata iri daban-daban har guda huɗu wadanda suka bambanta ta yanayin muninsu. Nau'i na ɗaya shi ne cire wani ɓangare ko kuma yanke ɗan-tsakar mace baki ɗaya. Nau'i na biyu shi ne cire wani bangare ko ɗan-tsakar baki ɗaya da lebban da ke ciki da kuma waɗanda suka kewaye farjin mace kuma wani lokaci yakan ƙunshi yanke fatar da ke gefen farjin.

Nau'i na uku ya ƙunshi sake ɗame bakin farji ta hanyar yanko wani ɓangaren farjin a yi amfani da shi a matsayin wani shamaki.

Nau'i na huɗu, wanda ya fi tsauri, ya ƙunshi cire ɗan-tsaka baki ɗaya, da duka sauran ɓangarorin farjin tare kuma da liƙe bakin farjin ta hanyar yi masa ɗinki.

A cikin shekaru biyun da suka gabata, likitocin sun fara faɗaɗa ilimi da dabaru kan tiyatar gyara barnar da kaciyar mata ke yi.

A cikin 2004, wani likita a ƙasar Faransa, Dokta Pierre Foldès ne ya gudanar da tiyatar gyara kaciyar mata ta farko. Tun daga wannan lokacin, wasu likitocin sun ɓullo da dabaru daban-daban na gudanar da tiyatar.

Amma, a Afirka, inda buƙata ke da yawa, babu damarmakin yin tiyata kai-tsaye. A halin yanzu ana samunsa ne kawai a Kenya inda marasa lafiya za su biya daga aljihunsu ko kuma a Masar, inda ƙungiyoyi masu zaman kansu za su iya biyan ɗaukar nauyin wasu mabuƙata.

A Turai wasu ƙasashe sukan yi tiyatar a kan farashi mai rahusa. A ƙasashe irinsu Belgium da Jamus da Faransa da Sweden da FInland da Switzerland shirin Inshorar lafiya ta gwamnati ta kan ɗauki nayin irin wanna tiyatarna jama'a ce ta sake ginawa a Belgium, Jamus, Faransa, Sweden, Finland da Switzerland. Ana samun hakan ma a ƙasar Netherlands.

A cewar wani ƙwararren likita na FGM a Kenya, tiyatar gyaran kaciyar ta kama hanyar zama wani fannin ƙwarewa na musamman a ɓangaren kiwon lafiya a wasu ƙasashen yamma.

"Akwai wasu likitocin fida na Turai da Amurka da ke yi wa al'ummomin ƙasashen waje," in ji Dokta Adan Abdullahi, wani likitan fiɗa da ke Nairobi.

“Amma ba kowane likitan fiɗa ne zai iya yin wannan tiyatar ba. Yana da rikitarwa kuma kowanne mai jinya ya bambanta.”

Dokta Abdullahi ya ce mata masu kowane irin kaciya za su iya amfana da tsarin, amma matan da suka fi samun sauki su ne wadanda abin ya yi matuƙar shafa.

"Yana da tasiri matuƙar tasairin kan haihuwa, musamman ga nau'in da ke tsuke bakin farji.'' in ji shi

Ya ce ana samun sauki kan batutuwa kamar su ciwo a lokacin jima'i, wani lokaci ma har a warke baki ɗaya bayan an yi tiyata za a iya inganta su sosai ko kuma warkewa bayan tiyata, ya kara da cewa a sau dayawa tiyatar tana ƙara ingancin rayuwar majiyyata.

Asalin hoton, Haja Bilkisu

Haja with her family after a trip to Sierra Leone in 2002.
Bayanan hoto, Wannan bayan Haja ta je Saliyo ne a 2002. An yi mata a yayin wannan tafiyar. An dauki hoton jim kaɗan bayan sun dawo Jamus.

'Wahalar da jiki'

Haja Bilkisu, ƴar kasar Jamus ce daga Saliyo, an yi mata tiyatar gyaran kaciya da dama. Ta shawarci sauran waɗanda abin ya shafa da su yi bincike sosai kan abin da kowace tiyata ta ƙunsa kafin su yanke shawara.

''Gyaran da ake yi a kan ɗan-tsaka ba kawai sake fito da shi ba ne'', in ji ta.

"Yawancin matan da aka yi wa kaciya suna da tabo, waɗanda kan sa fatar ta yi tauri, dole ne ku tattauna da likitan ku, ta yaya za a magance tabon? Me za ku yi don ƙarawa wurin laushi?"

Ta bayyana hakan ba wai yana da tasiri kan jima'i ba ne kawai har ma da haihuwa.

Duk tiyatar da aka yi wa Haja ya ɗauki kusan sa'o'i shida ana yi.

“Hakika yana da wahala. Za a yi ma ka allurar kashe raɗaɗi. Kuma dole ne ka sha magani daga baya. Sai da na yi jimillan makonni uku ba na iya tafiya ,” in ji ta.

Saboda wahalar da ke tattare da tiyatar, wasu likitoci suna sha'awar inganta hanyoyin da ba na tiyata ba.

Dr Reham Awwad ita ce wanda ta kafa wani asibiti a Masar, Restore, wanda aka kafa a shekarar 2020 don bayar na'ukan kula na musamman ga matan da aka yi wa kaciya.

Dokta Awwad ta ce ta samu ƙwarin gwiwar kafa cibiyar kula da lafiyar ne bayan ta yi karo da wata da aka yi wa kaciya a lokacin da take sanin makamar aikin likitanci. Wannan ya sa ta nemi ƙwararewa kan tiyatar don kula da waɗanda matsalar ta shafa.

Ta ce ko da yake tiyatar na iya kawo sauki, amma a wasu lokuta yankan yana da tsanani ta yadda ko da ingantattun hanyoyin tiyata, ba za a iya gyara ɓarnar da kaciyar ta yi ba.

"Tabbas bana tunanin tiyata ita ce abin da ta dace da kowa," in ji ta.

"A gaskiya mun rage yawan aikin fiɗar da ake yi."

Dr Awwad ta ce kusan rabin mutanen da asibitinta ke kula da su a yanzu suna amfani da magunguna ne a da ke ƙara gudanar jini a yankin madadin tiyata. Ana kuma duba lafiyar ƙwaƙwalwa domin kwantar da hankali domin inganta tunanin matan da aka yi wa kaciya a lokacin da zasu iya tunawa.

Ta bayyana cewa akwai wasu hanyoyin da za a iya gwadawa waɗanda ba na tiyata ba - irin su amfani da sinadarin plasma mai arziƙin platelet, matakin da ake amfani da shi yanzu a fannoni daban-daban na likitanci.

"Plasma na iya haifar da warkar da ciwo da haɓaka gudanar jini da rage kumburi a wuraren da aka yi wa allurar," in ji ta, kodayake ta yi gargaɗin cewa farashin waɗannan matakan yana nufin ba kowa ne da ke buƙata zai iya samun su ba.

Asalin hoton, BBC

Locator map of countries offering surgery in Africa and Europe
Bayanan hoto, A Turai akwai ƙasashen da tsarin inshorar lafiya ke ɗaukar nauyin tiyatar gyaran kaciyar mata

Sabon jiki

Ga waɗanda suka zaɓi yin tiyatar gyaran kaciyar mata, sakamakon zai iya zama mai sanya juyayi.

Ga Haja daga Saliyo, ta ɗauki lokaci kafin ta saba da sabon jikinta.

“A karon farko da na ga ɗan-tsaka na a zahiri abin ya ba ni mamaki kamar wannan ba nawa ba ne,” in ji ta.

“An yi mun kaciya ina da shekara takwas. Ban taɓa ganin wannan ɓangaren jikin nawa ba.

Yanzu da ta warke, Shamsa ta ce duk da basussukan da ake bin ta, ta yi farin cikin kashe wadannan kuɗaɗe domin a yi mata tiyatar.

Ta ce: “Lokacin da na warke, sai na koyi yadda zan yi rayuwa da sabon sabuwar farjina,” in ji ta.

"Amma yanzu na san yadda ake ji idan an zama cikakkiyar mace."

People are also reading