Home Back

Bayan Shekaru 13 Suna Tsammani, Gwamnati Ta Jiƙa Ƴan Fansho da Biliyoyi

legit.ng 2024/10/6
  • Gwamnatin jihar Zamfara ta biya yan fansho sama da 4,000 kudin da suka bi jihar bashi na tsawon shekaru
  • Wadanda aka biya kudin sun hada da tsofaffin malaman makaranta da ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar
  • Mai taimakawa gwamnan jihar kan harkokin yada labarai ya bayyana yadda aka raba kudin ka tsofaffin ma'aikatan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara karkashin gwamna Dauda Lawal ta biya tsofaffin ma'aikatan jihar kudi sama da biliyan 5 da suka bi jihar bashi cikin shekaru.

Gwamnan Zamfara
Gwamnan Zamfara ya biya 'yan fansho bashin da suke bin jihar. Hoto: Dauda Lawal Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya ce tsofaffin ma'aikatan sun bi jihar bashin kudin ne har tsawon shekaru 13.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sulaiman Bala Idris ya nuna cewa an biya kudin ne bisa tsarin mataki bayan mataki da kuma tantancewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin waɗanda suka samu kudin

Gwamnatin ta bayyana cewa tsofaffin ma'aikatan ƙananan hukumomi da malaman makaranta 2,209 ne suka samu karbar kudin.

Sannan a bangaren tsofaffin ma'aikatan jiha kuma an samu kimanin mutane sama da 1,642 da suka samu karbar kudin.

Kudin da aka biya ma'aikatan

Gwamnatin ta bayyana cewa tsofaffin ma'aikatan ƙananan hukumomi da malamai an biya su sama da naira biliyan 2 sauran kudin kuma ya tafi ga tsofaffin ma'aiktan jiha.

Har ila yau gwamnatin ta tabbatar da cewa wadanda aka biya kudin suna rukunin tsofaffin ma'aikatan ne da suka yi ritaya daga shekarar 2012 zuwa 2019.

Gwamnatin jihar ta ce biyan kudin yana cikin alkawuran da gwamnan jihar ya dauka na farantawa tsofaffin ma'aikatan Zamfara.

Gwamnati ta yi kira ga NLC

A wani rahoton, kun ji cewa, gwamnatin tarayya ta shirya dabarar hana kungiyar kwadago tafiya yajin aiki da take kokarin tsunduma.

Ministan yada labarai na kasa, Idris Muhammad ne ya yi kira ga kungiyar domin sake zama a teburin tattaunawa maimakon tafiya yajin aiki.

Hakan ya biyo bayan kasa samun daidaito tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya ne kan mafi karancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Asali: Legit.ng

People are also reading