Home Back

Dakarun MDD sun fice daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo

dw.com 3 days ago
Hoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta rufe babban ofishinta na Lardin Kivu a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo, yayin da take ci gaba da janye dakarunta daga kasar, sakamakon kazancewar rikici.

Dakarun farko na wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun fara isa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo a shekarar 2003, amma yanzu haka dakaru dubu goma sha biyar ne suka fara ficewa daga kasar, bayan da gwamnatin Kinshasa ta umarce su su bar kasar, sakamakon gaza yin katabus wajen kawo karshen rikicin.

Tun a karshen shekarar 2021 ne yankin arewacin Kivu ke fama da hare-haren 'yan tawayen M23 masu samun goyon bayan kasar Rwanda, inda suka kwace iko da mafi akasarin yankin.

People are also reading