Home Back

Hukumar Tace Finafinan Kano ta haramta finafinan da ke nuna dabanci da ‘yan daudu

premiumtimesng.com 2024/5/3
‘Dalilin da ya sa na soke lasisin Ali Nuhu, Zango, Gabon, Naziru da sauran ‘yan wasa, furodusoshi da mawaka ‘- Almustapha

Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta haramta kwata-kwata shirya finafinai masu nuna dabanci da kuma harkokin ‘yan daudu.

Shugaban Hukumar, Abba El-Mustapha ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da ya yi da wasu jiga-jigan harkar finafinan Kannywood a ranar Laraba.

Cikin wata sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai na hukunar, Abdullahi Sulaiman ya fitar kuma mai ɗauke da sa hannun sa a ranar Laraba ɗin, bayyana wa cewa Shugaban Hukumar ya shaida wa masu shirya finafinan Kano cewa lokaci ya yi da za a daina shirya duk wasu finafinai da suka ci karo da tarbiyya da kyawawan ɗabi’un al’ummar Jihar Kano.

El-Mustapha ya ce dokar jihar ce ta bai wa hukumar sa ƙarfin ikon soke finafinai masu ɓata tarbiyya.

Hukumar ta bai wa furodusoshi, daraktoci da sauran ‘yan fim watanni ɗaya, domin kintsawa kafin dokar ta fara aiki.

Wasu da suka yi fice a fagen fiwota finafinan dabbanci sun haɗa da Abale, Ibrahim Sinana, Tijjani Asase da sauran su.

Mawaƙi Ado Gwanja ya yi tashe a baya wajen fitowa a finafinan daudu. Daga baya ya watsar ya kama waƙa gadan-gadan.

People are also reading