Home Back

Amurka ta nemi Isra'ila ta faɗi sunayen ƴan Hamas da ta ce ta kashe a Gaza

bbc.com 2024/6/18
..

Amurka ta faɗa wa Isra'ila cewa dole ne ta "fayyace" al'amura dangane da harin sama da rahotanni ke cewa an kashe mutum 35 a wata makaranta da ke tsakiyar Gaza da safiyar ranar Alhamis.

Ƴan jarida sun shaida wa BBC cewa wani jirgin yaƙi ne ya harba makamai masu linzami guda biyu a saman wasu azuzuwa da ke sansanin ƴan gudun hijra da ke Nuseirat.

Dakarun Isra'ila sun ce sun ƙaddamar da wani hari "wanda ya kai inda aka nufa" a kan wani "wurin Hamas" da ke makarantar, to sai dai ofishin yaɗa labarai na gwamnatin Gaza da ke ƙarƙarshin Hamas ya musanta iƙrarin harin.

Amurka ta nemi Isra'ila ta fito fili ta nuna 'yan ƙungiyar Hamas ɗin da ta ce ta kashe kamar dai yadda sojin na Isra'ila suna bayar da sunayen mutum tara.

Isra'ila dai ta kan tantance masu tayar da kayar baya da take hara a hare-haren sama to sai dai Amurka ba kasafai Amurka ke umartar ta ta fayyace hakan ba.

Ƴan Isra'ila "sun shaida mana cewa akwai masu tayar da ƙayar baya 20 zuwa 30 da suke nema kuma za su bayyana sunayen waɗanda suka haƙƙaƙe sun kashe...", in ji mai magana da yawun ofishin cikin gida na Amurka, Matthew Miller.

A wani jawabin ga manema labarai, mai magana da yawun sojin Isra'ila, Daniel Hagari ya bayyana sunayen 'yan Hamas da mayaƙan Jihadi guda tara da ya ce an kashe a harin. Ya ce za su bayyana sunan ƙarin wasu bayan aikin "tantance su".

A Amurka, Mista Miller ya ce Amurka ta ga rahotanni da ke cewa yara 14 ne aka kashe a harin.

"Idan hakan gaskiya ne cewa yara 14 aka kashe, ba 'yan ta'adda ba ne," ya ce.

"Sannan kuma gwamnatin Isra'ila ta ce za ta saki ƙarin bayani dangane da wannan hari...Muna tsammanin za a yi gaskiya wajen bayyana bayanan."

Mace-macen baya-bayan nan sun zo ne mako guda bayan kashe mutum 45 a wani harin Isra'ila a birnin Rafah.

Ma'aikatar Lafita ta Gaza ta ce an kashe mutum 40 da suka haɗa da mata da ƙananan yara 14 da mata tara sanna kuma an jikkata mutum 74.

Babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijra a Falasdinu, Unrwa, Philippe Lazzarini ya ce aƙalla mutum 35 aka kashe sannan aka jikkata da dama.

Hukumar ta Unrwa ta ce mutum 6,000 ne suke neman mafaka a makarantar a lokacin.

Sakataren majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya soki harin.

..

Asalin hoton, reuters

People are also reading