Home Back

Mun Cafke ‘Yan Kwaya 50,901 Da Gurfanar Da 9,034 A Shekara 3 – Marwa

leadership.ng 2024/5/17
Mun Cafke ‘Yan Kwaya 50,901 Da Gurfanar Da 9,034 A Shekara 3 – Marwa

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Mohamed Buba Marwa ya bayyana cewa sun samu nasarar cafke ‘yan kwaya guda 50,901 da suka kasance masu aikata laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi tare da samu nasarar gurfanarwa da daure mutum 9,034 hadi da kamo sama da tan-tan 7,561 na haramtattun kwayoyi a cikin watanni 38 da suka wuce.

A cikin shekaru uku kuma, hukumar ta lalata da tarwatsa hekta 1,057.33348 na tabar wiwi a sassa daban-daban na Nijeriya a wani mataki na nuna aikin ba sani ba sabo kan yaki da miyagun kwayoyi da safararsu.

Sannan a cewarsa, wannan wani kyakkyawar sako ne ga masu mu’amala da miyagun kwayoyi da su gane cewa Nijeriya a yanzu ba za ta lamunci munanan ayyukansu ba.

Marwa ya shaida haka ne a ranar Litinin a Legas yayin da ke jawabi wajen kaddamar da mika ofishin da Gwamnatin Burtaniya ta gina domin agaza wa kokarin hukumar NDLEA na cigaba da yaki da masu mu’amala da miyagun kwayoyi da dakile safaran miyagun kwayoyi a Nijeriya.

A cewarsa, “Mun hadu a nan ne ba kawai domin mu kaddamar da sabon ginin ofishi ba, har ma da mu yi murna kan irin nasarorin da muka cimma kan yaki da muke yi da masu ta’anmuli da miyagun kwayoyi da safararsa. A yau, da wannan kaddamar da sabon ofishin da gwamnatin Burtaniya ta yi da nufin karfafa wa kokarinmu wajen ci gaba da dakile amfani da miyagun kwayoyi.

“Dole ne na jinjina da mika godiyarmu ga gwamnatin Burtaniya bisa wannan gagarumin gudunmawa da ta mana. Kuma, da kyakkyawar hadin guiwa da ke tsakani za mu samu nasarar ci gaba da dakile ayyukan ‘yan ta’adda da tsarkake Nijeriya daga ta’anmuli da miyagun kwayoyi hadi da jigilarsu.

“Wannan ofishin aikin ba kawai an gina domin gudanar da aiki zalla ba ne, zai kuma kyautata dangantaka a tsakanin kasashen biyu wajen ci gaba da yaki da safaran miyagun kwayoyi.”

A cewarsa, alfanun da sabon ofishin zai musu na da matukar yawa da suka hada da bincike, bibiya da kuma sanya ido kan miyagun kwayoyi da ake jigilarsu domin dakile aniyar masu mu’amala da su.

“Mun kama kilogiram 7,560,748.5 (Tan 7,561), ba kawai dakile miyagun kwayoyi ba ne har ma da toshe wa masu jigilar aniyarsu na rabawa a inda suke son rarrabawa. Mun kuma samu nasarar tarwatsa hekta 1,057.33348 na gonar tabar wiwi a cikin shekaru uku da suka wuce,” ya shaida.

Duk da kyautar ofishin, shugaban hukumar ya kuma sake neman hadin guiwar gwamnatin Burtaniya domin kara kyautata himma wajen yaki da matsalar sha da fataucin miyagun kwayoyi a tsakanin kasashen biyu.

A cewarsa, ba za su bari a yi sako-sako da wadanan nasarorin da suke samu ba, ya nemi jami’ansa da su kara himma wajen shiga lungu da sako domin dakile aniyar masu sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Da yake jawabinsa a wajen taron, mataimakin wakilin Burtaniya a Nijeriya, Jonny Badter, ya ba da tabbacin gwamnatin kasarsu na ci gaba da taimaka wa NDLEA da Nijeriya a bangarorin yaki da fataucin miyagun kwayoyi da sauran muhimman bangarori.

Ya kuma nuna farin cikin gwamnatin Burtaniya kan yadda NDLEA ke samun gagarumin nasara wajen yaki da masu sha da masu fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya, ya ce kofarsu a bude take wajen ci gaba da taimaka wa Nijeriya.

People are also reading