Home Back

Abu shida da za ku yi don ku sa kanku farin ciki

bbc.com 2024/5/5
...

Asalin hoton, Getty Images

Motsa jiki da cin lafiyayyen abinci za su zama abin da zai kara wa mutum farin ciki. Sai dai ba su kadai ne ke saka farin ciki ba.

Dr Michael Mosley, wakilin BBC, ya bayyana ra’ayinsa kan abubuwan da za su saka mutane farin ciki a cikin wani shirin rediyo na BBC.

Wadanne karin abubuwa ne za mu koya da za su saka mu rayuwa cikin farin ciki? Ga wasu daga ciki wadanda za su kara muku farin ciki.

1- Rubutu

Idan kana da tarin bayanai a kanka, za ka yi mamakin gano cewa wadanne daga ciki ke da muhimmanci ta hanyar rubuta su a takarda.

Idan za ka ware minti 15 ka yi tunani, za ka iya rage tarin abubuwa da kuma gajiya da ke tattare da kai. Farin cikin ka zai karu.

Za ka yi barci cikin nishadi. Garkuwar jikinka za ta karu. Kwakwalwarka ma za ta samu lafiya.

2- Yin nesa da waya

Watakila kun sani cewa amfani da waya da yawa zai shafi lafiyar kwakwalwarku.

Za ta shafi barcin ku da kuma kuzari. Abu mai wuya ne a daina dogaro da waya kwata-kwata.

Saboda yawancin abun da muke so a kowace rana yana alaka da waya.

Wani bincike da aka gudanar a Jamus ya gano cewa mutanen da ke amfani da wayoyinsu na sa’a daya a rana, suna rayuwa cikin farin ciki ba tare da gajiya ba.

Idan kana son rage yawan lokaci da kake dauka wajen amfani da wayarka, ajiye ta a wani daki na daban zai iya zama abu mai kyau.

3- Sayen shuka a ajiye a gida

...

Asalin hoton, Getty Images

Shuka sirrai a gida ba wai kara wa gida kyau kadai suke yi ba, suna kara ingancin iska da kuma jin dadi.

Haka ma, suna kara tunani mai kyau da kuma kuzarin yin aiki. Samar da shuka a gida zai iya saka mutum ya yi numfashi mai tsawo.

Dangane da haka, kwakwalwa na samun karin iska da kuma barci mai kyau. Akwai alamun cewa zaman lafiya ya samu.

Wani bincike ya nuna cewa idan aka cire shuka daga ofis, hakan na karawa ma’aikata gajiya, karfin aiki da kuma mayar da hankali ga aiki shi ma zai ragu.

Haka ma, wani bincike ya gano cewa karfin aikin ma’aikata yana karuwa da kashi 19 idan ya kasance suna ganin shuka a kusa da su.

4- Rera waka

...

Asalin hoton, Getty Images

Za ka ji dadin rera waka idan kana wanka ko kuma sauraron wakoki a rediyo yayin da kake tafiya a mota.

Hakan yana fitar da wasu sinadari daga jikinka da za su sa ka farin ciki.

Haka kuma, waka yana da hanyoyi daban-daban da yake shafar jikin mutum.

Yana kara wa mutum kwarin gwiwa, rage kadaici da kuma kaucewa gajiya.

5- Koyon wani abu sabo

Idan kana cikin gajiya, kara yawan abubuwa da za ka yi na kara maka gajiya.

Akwai hujjoji da ke nuna cewa koyon wani abu sabo zai taimaka wajen gajiya da kuma kwanciyar hankali.

Idan ka fara koyon wani abu sabo, ka mayar da hankali kacokan a kansa.

A wancan lokaci dukkan hankalinka na kan abun. Hakan na kwantar da hankalin kwakwalwa.

Yana kuma taimaka maka wajen duba dabi’unka. Hakan na nufin cewa ba sai ka yi tunani da yawa ba kan halayenka.

6- Wadanne abubuwa ke saka ka farin ciki?

Dukkan wannan zai zama kaman bambara-kwai, akwai bayani na kimiyya kan hakan. Abin farin ciki ne gode wa mutanen da suka taimaka maka, ko da karamin taimako ne.

Wannan zai inganta kwakwalwarka.

Domin samun farin ciki, ka fara sauya tunanin da kake yi daga mara kyau zuwa mai kyau.

Ka yi tunanin abu guda uku da suka sa ka farin ciki a yau. Zai iya zama komai.

Ka gode wa mutane ko kuma ka tattauna kan muhimman abubuwa da su.

People are also reading