Home Back

Kotu a Maiduguri ta yanke wa Ibrahim hukuncin ɗauri bisa laifin handame naira Miliyan 12 dukiyar Marayu

premiumtimesng.com 2024/5/19
Kotu a Maiduguri ta yanke wa Ibrahim hukuncin ɗauri bisa laifin handame naira Miliyan 12 dukiyar Marayu

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa EFCC ta gurfanar da Isiyaku Ibrahim gaban alkali Umaru Fadawu na babban kotu dake Maiduguri jihar Barno kan zargin handame wa wasu marayu gadon su har naira miliyan 12.

Hukumar ta kama Ibrahim ranar 3 ga Yuli 2023.

Bisa ga karar da hukumar ta shigar ya nuna cewa Isyaku Ibrahim da wani Mallam Ibrahim daga shekarar 2014 zuwa 2019 a layin Jajere Baga sun yi sama da fadi da naira miliyan 12 kudaden magada.

Takardar karar ya nuna cewa naira miliyan 12 din magadan marigayi Muhammad Isiyaku sun hada da gidaje uku, filaye biyu da aka katange da daya an gina shaguna bakwai a ciki, gidajen buredi biyu, fili daya da ba a katange ba, motocin ɗaukar mai, wato tankuna biyu da na’urar ganareta babba daya.

Tun da aka mika wa Ibrahim dukiyar waɗannan marayu ya rika facakarsa kamar ta sa.

A kotun Ibrahim ya musanta laifukan da ake zarginsa da su Wanda hakan ya sa lauyan dake kare marayun Faruqu Muhammad ya gabatar da shaidu shida da takardu da dama da suka nuna cewa ya aikata laifukan.

Alkali Fadawu ya yanke wa Ibrahim hukuncin zaman kurkuku na shekara daya ko ya biya taran naira 100,000 bisa laifin yin sama da fadi da dukiyar marayu.

People are also reading