Home Back

Gwamnati tarayya ta yi wa wasu ma’aikata ƙarin albashi

premiumtimesng.com 2024/5/18
Tinubu ya rattaba hannu kan sabon kudirin ba da lamuni na dalibai

Gwamnatin Tarayya ta bayyana sanarwar za ta yi ƙarin albashi ga wasu ma’aikatan ta masu karɓar albashi a tsarin karɓar albashin ɓangarorin ma’aikata 6.

Akwai waɗanda aka ƙara wa kashi 25 bisa 100 na albashin su, akwai kuma waɗanda aka ƙara wa kashi 35 bisa 100.

Amma wannan ba ya cikin ƙarin albashin da ƙungiyar ƙwadago ke nema a yi, wanda ta ke kan tattaunawa da gwamnatin tarayya, tun bayan cire tallafin fetur.

Kakakin Yaɗa Labaran Hukumar Tantance Albashi ta Ƙasa (NSIWC), Emmanual Njoku ne ya bayyana haka, a ranar Talata, a Abuja.

Waɗanda aka yi wa wannan ƙarin albashi su ne ma’aikatan da ke karɓar albashi a ƙarƙashin tsarin CONPSS, CONRAISS da CONPOSS. Waɗannan na uku su ne ‘yan sanda.

Akwai kuma COPASS, CONICCS da CONAFSS.

“Amma ƙarin albashin zai fara ne tun daga ranar 1 ga Janairu.” Inji Njoku.

Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta kuma yi ƙarin kuɗin fansho na tsakanin kashi 20 zuwa 28 bisa 100 ga masu karɓar fansho a ƙarƙashin tsarin DBS. Su ma ƙarin na su zai fara ne daga 1 ga Janairu.

Njoku ya ce an yi wannan ƙarin bisa tsarin doka ta Sashe na 173 ta Kundin Dokokin Najeriya.

Ya ce waɗanda ke aiki a manyan makarantun gaba da sakandare da waɗanda ke ɓangaren kiwon lafiya na tuni har sun fara karɓar na su ƙarin albashin.

Wato ya na nufin masu karɓar albashi a tsarin CONUASS da CONTISS. Sai kuma ‘yan tsarin CONPCASS da CONTEDISS.

A ɓangaren kiwon lafiya akwai irin su CONMESS da CONHESS, inji Njoku.

Ya ce kuma ana ci gaba da tattaunawa tsakanin NLC, TUC da gwamnatin tarayya, domin yi wa sauran ba’arin ma’aikatan gwamnatin tarayya ƙarin albashi.

NLC da TUC dai na neman gwamnatin tarayya ta yi wa ma’aikata ƙarin albashi daga Naira 30,000 mafi ƙanƙantar albashi zuwa Naira 615,000 mafi ƙanƙantar albashi, domin cire tallafin fetur ya ruguza tsarin tattalin arzikin kowane ɗan Najeriya.

People are also reading