Home Back

Mutane miliyan 783 za su fuskanci matsananciyar yunwa a kasashe- MDD

rfi.fr 2024/4/28

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya koka da yadda mutane akalla miliyan 783 za su fuskanci matsananciyar yunwa a bana sakamakon gazawa wajen samar da abinci da ya fuskanci koma-baya da kashi 19 da ke matsayin tan biliyan 1 da miliyan 50 na abinci.

Wallafawa ranar: 28/03/2024 - 13:20

Minti 1

Wani aikin rarraba kayan abinci a birnin Bangui na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.
Wani aikin rarraba kayan abinci a birnin Bangui na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya. © Carol Valade/RFI

Rahoton wanda majalisar ta fitar a jiya Laraba, ya koka da cewa idan har aka ci gaba da samun raguwar abinci da kasashe ke samarwa ko shakka babu ba a iya cimma muradin wadata duniya da abinci nan da shekarar 2030.

Rahoton ya ce yanayin samar da abinci ya ragu da kashi 17 a shekarar 2021 fiye da yadda aka gani a shekarar 2019.

Rahoton ya alakanta yakin Rasha a Ukraine da kuma hare-haren Isra’ila a Gaza a matsayin wani dalili da ya ta’azzara karancin abincin, haka zalika halin da aka shiga a Haiti.

A cewar rahoton Majalisar Dinkin Duniyar, matsaloli masu alaka da rikici da ke kan hana noma a kasashe da dama ya taka muhimmiyar rawa wajen haddasa karancin abincin matsalar da rahoton ke cewa za ta fi tsananta a Afrika.

Tun gabanin rahoton na baya-bayan nan Bankin Duniya da shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniyar WFP sun yi gargadin tsanantar yunwar a yankin kuryar gabashin Afrika, da kuma wasu kasashe na yammacin nahiyar.

 
People are also reading