Home Back

Tsohon Gwamna, Malam El-Rufa'i Ya Bayyana Babbar Matsala 1 Tak da Ta Addabi Najeriya

legit.ng 2024/5/19

Jihar Borno - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya ce shugabanci shi ne babbar matsalar Najeriya.

El-Rufai ya bayyana haka ne a jawabinsa a wurin taron karawa juna ilimi na manyan jami’an gwamnatin jihar Borno wanda ya gudana ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu.

Malam Nasiru El-Rufai.
Gazawar shugabanci ne babbar matsalar Najeriya in ji El-Rufai Hoto: Nasiru El-Rufai Asali: Facebook

Taron wanda aka yi wa taken, "inganta kwarewar jami'an gwamnati wajen aiwatar da manufofi da sarrafa albarkatu," ya gudana ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Mallam El-Rufai, babban baƙo mai jawabi a taron bitar, yace ya ziyarci jihar Kaduna sau biyar ne kawai tun bayan sauka daga mulki kusan shekara daya da ta wuce.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, tsohon gwamnan ya ce ya yi haka ne saboda ba ya son sukar shugabanni, na yanzu ko waɗanda suka shuɗe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Abin da muka rasa shi ne jagoranci na gari, babban abin da ke kawo kyakkyawan shugabanci. Wajibi kowane shugaba ya zakulo mutane masu gaskiya domin sauke nauyin da aka ɗora masa.

"Muna iya hangen cewa matsala ɗaya ce ta zame wa Najeriya ƙarfen ƙafa, ba rashin abinci, yunwa, hauhawar farashin canji ko cire tallafin mai bane, matsalar ita ce gazawar shugabanci.

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa duk kirki da nagartar shugaba ba zai yi tasiri ba matuƙar bai jawo mutanen azziƙi sun kewaye shi a gwamnati ba.

El-Rufai ya ce ya ji dadin abubuwan da ya gani a Maiduguri da wasu sassan Borno, inda ya ce wuraren sun yi kyau duk da rikicin Boko Haram da aka kwashe sama da shekaru goma ana yi.

A wani rahoton kuma

Asali: Legit.ng

People are also reading