Home Back

Jam’iyyar NNPP ta dakatar da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf

dalafmkano.com 2024/5/18

Tsagin jam’iyyar NNPP ta ƙasa karkashin jagorancin Major Agbo, ya sanar da dakatar da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf daga cikin jam’iyyar.

A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar ta ƙasa Ogini Olaposi, ya fitar a yayin taron ‘yan jarida a Talatar nan a Abuja, tsagin jam’iyyar ta NNPP, ya ce rashin bayyana a gaban kwamitin ladabtarwar jam’iyyar da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi shine ya sanya su ɗaukar wannan mataki.

Ya ƙara da cewa matakin na zuwa ne sakamakon fusata da jam’iyyar ta yi kan halartar wani babban taron jam’iyyar da gwamnan ya yi wanda tsagin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya jagoranta a ranar 6 ga watan Afrilun nan na shekarar 2024. kamar yadda jaridar THE PUNCH ta rawaito.

Sai dai tuni wasu ƴan Kwankwasiyyar suka yi watsi da wannan dakatarwa.

Dambarwar dai na zuwa ne yayin da itama jam’iyyar APC, ke ci gaba da fuskantar ta ta dambarwar, musamman ma da aka jiyo yadda wani sashi na shugabancin jam’iyyar a mazaɓar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, aka jiyo shi ya dakatar da shugaban riƙo na APC ta ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, daga cikin jam’iyyar.

Sai dai daga bisani shugabancin jam’iyyar ta APC, a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, ya musanta batun dakatarwar lamarin da yace ma ana shirye-shiryen ɗaukar mataki akan waɗanda suka bayyana dakatarwar.

People are also reading