Home Back

MATSALAR TSARO: ‘Yan bindiga sun yi wa masarauta takakkiya, sun bindige basarake sun fice

premiumtimesng.com 2024/5/20
Yadda ‘yan bindiga suka sace dimbin fasinsoji a tashar jirgin kasa, suka ji wa mutane rauni

‘Yan bindiga sun yi takakkiya har cikin masarautar yankin Umuike da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Akaeze Ivo a Jihar Ebonyi, inda suka bindige Basarake Umazi Ubani.

An bindige Ubani lokacin da wasu ‘yan ta-kifen suka mamaye masarautar sa,a ranar Juma’a.

PREMIUM TIMES ta ji cewa maharan sun buɗe wuta sosai lokacin da suka isa masarautar.

Hakan ya tilasta mazauna yankin firgita, suka arce domin tsira da rayukan su.

Kodinetan Kungiyar Ci-gaban Akaeze maiauna Chinasa Okorie, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya yi tir da kashe basaraken, wanda ya nuna cewa mutumin kirki ne da zai yi wahala a samu wani basarake mai kirki kamar sa.

“Wajen ƙarfe 10 na ranar Juma’a da dare, sai aka kira ni, aka ce min ana harbe-harben bindiga a fadar basaraken mu. Bayan ƙura lafa, sai aka gano sun kashe shi.”

Ya ce jami’an tsaro ne kaɗai za su iya cewa ga waɗanda ke da hannu a kisan.

Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi, Joshua Ukandu, ya ce sun fara farautar waɗanda suka kai harin.

People are also reading