Home Back

Yan Sama Jannatin Shenzhou-17 Sun Dawo Doron Duniya

leadership.ng 2024/5/17
Yan Sama Jannatin Shenzhou-17 Sun Dawo Doron Duniya

A yau Talata, ‘yan sama jannati 3 dake cikin kumbon Shenzhou-17 na kasar Sin da suka hada da Tang Hongbo da Tang Shengjie da kuma Jiang Xinlin, sun fito daga cikin sashen komawa na kumbon da ya sauka a tashar saukar kumbuna ta Dongfeng dake yankin Mongolia ta Gida mai cin gashin kansa a arewacin kasar Sin.

Hukumar kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta ce dukkan ‘yan sama jannatin 3 suna cikin koshin lafiya kuma sun kammala aikinsu cikin nasara. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

People are also reading