Home Back

Mai ra'ayin kawo sauyi ya lashe zaɓen Iran

bbc.com 2024/8/23
.

Asalin hoton, REX/SHUTTERSTOCK

Ɗan takara mai ra'ayin kawo sauyi a Iran Masoud Pezeshkian ya lashe zaben shugaban kasar Iran.

Ya ba wa mai bi masa baya Saed Jalili na jam'iyar masu ra'ayin mazan jiya tazarar sama da kuri'a miliyan uku a zagaye na biyu na zaben da aka gudanar jiya Juma'a.

Ya samu kuri'a miliyan 16, cikin miliyan 30 da aka kada a zaben da mutane da dama suka kauracewa.

Magoya bayan Mista Pezeshkian sun yi ta murna a birnin Tehran, da sauran sassan ƙasar, tunda muku-mukun safiya.

Masu aiko da rahotanni sun ce jama'a da dama a Iran sun yi imanin cewa nasarar da masu neman sauyi suka samu ba abu ne da jagoran juyin juya halin Musulunci kasar Ayatullah Ali Khamenei zai so ba.

An gudanar da zagayen farko na zaɓen ranar 28 ga watan Yuni. Mutum miliyan 61.1 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'arsu a zaɓen.

Ranar juma'ar nan ne aka gudanar da zagaye na biyu, wanda yanzu aka samu wanda ya yi nasara

An bi tsauraran matakai wajen tantance ƴan takarar shugabancin ƙasar da suka fafata a zaɓen, hakan ya kai ga haramta wa wasu manyan ƴan siyasa shiga takarar.

Mutum shida ne kawai suka samu nasarar tsayawa takarar, kuma biyu daga cikinsu sun fice daga takarar kwana biyu kafin zaɓen.

People are also reading