Home Back

Gudunmawa 10 Da Ilimi Ke Bayarwa Ga Al’umma (2)

leadership.ng 2024/7/3
Gudunmawa 10 Da Ilimi Ke Bayarwa Ga Al’umma (2)

A kowane lokaci, ilimi na samun tagomashi da kuma girmamawa daga wurin al’umma. Masu ilimi, su ne ke samun ingantacciyar rayuwa, wadda kowa da kowa ke sha’awa ko mararin samun irin ta.

Idan mutane suka karanci bangaren fannonin da ake ribibin su wajen daukar ma’aikata, ko shakka babu suna samun albashi mai matukar tsoka, ta yadda za su taimaki kansu da iyayensu da sauran danginsu baki-daya.

Har ila yau, ilimi na sa a samu daukaka; wadda ba a taba zato ba, sannan yana taimakawa wajen cimma kowane irin buri na rayuwa.

Bugu da kari, ilimi na bayar da dama wajen samun kudaden da za su taimaka wa mutum a rayuwarsa ta yau da kullum tare kuma da samun farin ciki ta fuskoki daban-daban.

6- Masu Ilimi Na Matukar Taimaka Wa Al’umma 

Ta wace hanya masu ilimi ke taimaka wa al’umma? Kasancewar masu ilimi, sun san muhimmancinsa tare kuma da sanin abin da ya kamata, shi yasa a duk inda suka fi yawa ake samun zaman lafiya da hadin kai da kuma rayuwa mai inganci.

Haka nan, abu ne mai dadi mutum ya kasance cikin al’umma, wadda ta san martaba da taimakon junanta tare da kai wajen ciyar da al’umma baki-daya gaba.

Sannan, a duk wurin da masu ilimi ke da rinjaye, suna kokarin taimaka wa masu karamin karfi, musamman ta bangarorin da suka gaza, don su ma su samu farin ciki da walwala a tasu rayuwar.

7- Samar Da Al’umma Mai Tafiya Daidai Da Zamani 

Ilimi shi ne babban jagoran ci gaban al’umma, don haka ya kamata mutum ya yi kokari ya san abubuwan da suka shafi al’adunsa, tarihi da kuma sauran al’amuran da suka shafe shi kai tsaye.

Haka zalika, a koda-yaushe ilimi na tafiya ne da zamani; shi yasa masu ilimi ba a taba barin su a baya, wajen rungumar sabbin abubuwan da zamani ke dauke da su.

Har ila yau, kamar yadda kowa ya sani ne cewa, ilimi haske ne; sannan kuma wata kofa ce ta fahimtar dukkanin wasu al’amuran rayuwa.

8- Mu’amala Daban-daban

Ilimin fasahar zamani, na taimakawa wajen hada mutane da kamfanoni daga ko’ina a fadin duniya ba tare da wata katanga ba, muddin dai za a iya yin mu’amala tare da yin musayar ra’ayi da mutane daga wasu kasashe masu al’adu mabambanta, wannan kai tsaye yana nuni ne da irin muhimmancin da ilimi yake da shi.

Sa’annan, ilimi yana matukar taimaka mana wajen sanin juna da yin mu’amala ta kai tsaye, duk kuwa da irin banbance-banbancen da ke tsakaninmu.

9- Samar Da Damar Taimakawa 

Gudunmawar da ilimi ke bayarwa a tsakanin al’umma, na da matukar yawa; duba da cewa, a irin wannan zamani babu wani abu da zai iya yiwuwa ba tare da ilimi ba.

Idan muka dubi bangaren shugabanci, sanin kowa; babu yadda za a yi jahili ya jagoranci al’umma, koda kuwa a Karkara ne; ballantana kuma a Birane.

Haka nan, batun kasuwanci a halin yanzu; musamman yadda duniya ta canja, kusan komai ya zama na ilimi. Don haka, da zarar ka kasance a matsayin jahili; akwai kasuwanci da dama da zai fi karfinka, sai dai ka zama dan kallo.

10- Daga Darajar Dan’adam

Ko shakka babu, babu abin da ke mayar da Dan’adam ya zama cikakken mutum; tamkar Ilimi, domin kuwa wani mabudi ne wanda ke mayar da mara karfi ya zama mai karfi, wanda ba dan kowa ba; ya zama ya gagara a tsakanin al’umma, sakamakon wannan ilimi da yake da shi.

Har ila yau, ilimi ne kadai zai mayar da dan talaka ya zama wani mashahurin malami ko mai mulki ko kuma wani mai fada a ji.

Hakan ya sha faruwa a tsakanin al’umma, domin kuwa ana samun shugaban kasa, gwamna, sanata, minista da sauran makamantansu, wanda dan talakawa ne kowa ya sani; amma darajar ilimi ta ba shi wannan daukaka.

People are also reading