Home Back

Ingila za ta buga wasan sada zumunta da Bosnia ba ƴan wasa shida

bbc.com 2024/7/5
England

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Litinin tawagar ƙwallon kafa ta Ingila za ta buga wasan sada zumunta da Bosnia-Herzegovina ba tare da ƴan wasa shida ba.

Za ta yi wasan ne ba tare da wasu masu tsaron bayanta ba da suka hada da Harry Maguire da Luke Shaw da kuma John Stones.

Ɗan wasan Manchester United, Maguire da Shaw suna jinya, kuma koci, Gareth Southgate ya ce da ƙyar ne idan za su fuskanci Iceland a wani wasan sada zumuntar ranar Juma'a.

Stone bai samu zuwa sansanin horon tawagar Ingila da wuri ba, kenan baya kan ganiya, shi kuwa Anthony Gordon na jinya, yayin da aka bukaci Bukayo Saka ya huta.

Shi kuwa Jude Bellingham zai koma cikin tawagar Ingila ranar 8 ga watan Yuni, bayan da ya lashe Champions League a Real Madrid ranar Asabar a Wembley.

Ana sa ran Bellingham zai zama tauraro a Euro 2024, bayan da ci kwallo 23 a dukkan fafatawa a bana da lashe ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon La Liga na 2023/24.

Wasan sada zumunta da Ingila za ta yi a St James Park da kuma Wembley, shi ne na karshe da tawagar za ta yi daga nan ta je Jamus ranar 14 ga watan Yuni, domin shiga Euro 2024.

Ingila za ta fara wasan farko a gasar ta cin kofin nahiyar Turai da Serbia ranar 16 ga watan Yuni.

Tawagar da Southgate ke jan ragama, wadda ake sa ran za ta taka rawar gani a Euro 2024 tana rukuni na uku da ya hada da Slovenia da Denmark da kuma Serbia.

People are also reading