Home Back

Ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da sayar da Burtalai a wasu garuruwan ta

dalafmkano.com 2024/5/19

Biyo bayan kokawar da wasu Fulani Makiyaya suka yi kan yadda wasu suka gididdiba burtalai yayin da aka siyarwa Manoma, a garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, yanzu haka ƙaramar hukumar Tofa ta dakatar da taɓawa, ko kuma sayar da dukkanin Burtalan kiwon shanun ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban riƙon ƙaramar hukumar ta Tofa Abubakar Sulaiman Mai Rogo, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da aka aikowa Dala FM Kano, a ranar Alhamis.

Mai Rogo, ya kuma ce ƙaramar hukumar ba ta da hannu a kan taɓa dukkan guraren, a dan haka sun dakatar da dukkanin yunƙurin taɓa Burtalan har sai shugabanni na kwamitin ƙasa sun kammala bincike wanda yanzu haka ake ci gaba da yi.

Da yake nuna jin daɗin sa kan matakin dakatarwar, amadadin Fulanin garuruwan, shugaban ƙingiyar Funali Makiyaya ta Gan Allah, Ahmad Shehu Gajida, yabawa gwamnatin jihar Kano, da kuma ƙaramar hukumar ta Tofa ya yi, bisa karɓar koken su da suka akai.

A baya-bayan nan ne dai a zantawar Dala FM Kano, da wasu Funalani Makiyaya mazauna garuruwan Yanoko da Gajida da kuma Dindere, suka koka kan yadda aka gididdiba burtalan a yankunan nasu aka siyarwa manema, lamarin da suka ce ka iya sawa su rasa guraren da za suyi kiwon shanun su wanda hakan babbar barazana ce a gare su.

People are also reading