Home Back

Tsananin Zafi: Gwamnatin Saudiyya ta dakatar da jifan shaidan a Jamrat tsakanin karfe 11 na safe zuwa 5 na yamma

premiumtimesng.com 2024/7/6
Tsananin Zafi: Gwamnatin Saudiyya ta dakatar da jifan shaidan a Jamrat tsakanin karfe 11 na safe zuwa 5 na yamma

Hukumomin Saudiyya sun saka dokar hana zuwa jifan Shaidan Jamrat na wucin gadi tsakanin karfe 11 na safe zuwa 5 na yamma saboda tsananin zafi.

A cewar wata sanarwa da ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta fitar, wadda hukumar alhazai ta Najeriya ta raba a Muna a ranar Litinin din da ta gabata, an samu karuwar mace-mace masu nasaba da zafi a cikin sa’o’i 48 da suka gabata, lamarin da ya sa aka dauki wannan mataki domin kiyaye lafiyar mahajjata.

A dalilin haka gwamnatin ta umarci Alhazai su rika zama a gida daga karfe 11 na rana zuwa ƙarfe 4 na yamma lokacin gari ya ɗanbyi sany-sanyi.

Ana ta samun rasuwar mutane sanadiyyar tsananin rana da ake yi a musamman Makka da Madina.

Ƙasar Jodan ta bayyana cewa alhazai 14 ne suka rasu ƴan asalin ƙasar a Saudiyya, haka ita ma ƙasar Iran, ta bayyana wa kafafen yaɗa labarai cewa mutum 5 ƴan asalin ƙasarta sun rasu a kasar Saudiyya sanadiyyar tsananin Zafi.

An samu rahoton rasuwar Alhazai da dama a kasar na Saudiyya. Wasu ba a bada rahoton su ba wasu kuma ana tantance su.

People are also reading