Home Back

Ana Cikin Rikicin Sarauta, Gwamna Abba Ya Juyo Kan 'Yan Daba a Kano

legit.ng 2024/7/3
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya nuna damuwarsa kan yadda ayyukan ƴan daba ke ƙara yawaita a wasu sassan birnin Kano
  • Gwamnan ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da su ɗauki mataki mai tsauri kan ayyukan dabanci a jihar
  • Abba Kabir Yusuf ya kuma yi kira ga alƙalai da su guji saurin sakin mutanen da aka samu da laifin aikata ayyukan daba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga jami'an tsaro da su ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan ayyukan dabanci a jihar.

Gwamna Abba ya nuna damuwarsa kan yadda ayyukan ƴan daba suka ƙara yawaita a wasu sassan birnin Kano.

Gwamna Abba ya fusata kan ayyukan 'yan daba
Gwamna Abba ya bukaci jami'an tsaro su dauki mataki kan 'yan daba Hoto: Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

Ayyukan ƴan daba na ƙaruwa a Kano

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a shafin Facebook a ranar Asabar, gwamnan ya nuna rashin amincewarsa kan yadda faɗace-faɗace tsakanin ƴan daba ke ƙaruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya kuma nuna muhimmancin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi tare da jami'an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.

"Gwamnati ba za ta tsaya ta zura ido wasu ɓata gari su lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin da mutanen jihar mu masu bin doka da oda suke samu ba."
"Muna aiki tuƙuru tare da jami'an tsaro domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al'ummarmu a kowane lokaci."

- Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba ya yi kira ga alƙalai

Da yake magana kan alƙalai, gwamnan ya yi gargaɗi kan sakin mutanen da aka samu da aikata daba ba tare da sun fuskanci hukunci ba.

"Ya kamata alƙalai su fahimci barazanar da waɗannan ƴan daban suke yiwa walwalar al'ummarmu tare da tabbatar sa cewa sun yi hukunci cikin adalci."

- Abba Kabir Yusuf

Ƴan daba sun tuba a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ce kimanin tubabbun ƴan daban 200 a jihar ne yanzu haka suka zama ƴan ƙasa na gari.

Gwamna Abba Kabir ya ce ce daga cikin waɗanda rundunar ƴan sandan Kano ta kama kimanin 200, akwai ɓarayin waya da ƴan bangar siyasa, kuma dukkanninsu yanzu suna bayar da gudummawa wajen ci gaban Kano.

Asali: Legit.ng

People are also reading