Home Back

Sanusi Vs Aminu: 'Yan Majalisa 12 Na Majalisar Kano Sun Yi Mubaya'a Ga Sarki Na 15

legit.ng 2024/7/5
  • Mambobi 12 na majalisar dokokin jihar Kano sun yi mubaya'a ga sarki na 15, Aminu Ado Bayero a ƙaramar fadar Nasarawa
  • Ƴan majalisar na jam'iyyar APC sun ziyarci basaraken a fadar da yake zaune ranar Talata, 28 ga watan Mayu, 2024
  • Wannan mataki da suka ɗauka na zuwa ne a lokacin da rikicin sarautar Kano ya buɗe sabon babi bayan kotuna sun bayar da umarni daban-daban

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Yayin da rigimar sarauta ke ƙara ƙamari a jihar Kano, ƴan majalisa 12 na APC a majalisar dokokin jihar sun yi mubaya'a ga sarki na 15, Aminu Ado Bayero.

Bisa jagorancin shugaban marasa rinjaye, Labaran Abdul Madari, mambobin majalisar na APC sun kai ziyara ga Aminu Ado a ƙaramar fadar Nassarawa.

Aminu Ado Bayero.
Yan majalisar APC a Kano sun marawa Aminu Ado Bayero baya Hoto: Aminu Ado Bayero Asali: Facebook

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ƴan majalisar sun ziyarci basaraken ne jim kaɗan bayan fitowa daga zaman majalisar dokokin Kano ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba rikicin sarauta ya ɓarke tun lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16.

Sanusi II da Aminu Ado Bayero dai sun ki amincewa da matsin lamba daga umarnin kotu daban-daban na neman su fice daga fadar sarkin da suke zaune.

Yayin da ‘yan majalisar APC a majalisar dokokin jihar suka kai ziyara ga Aminu Ado Bayero ba, kungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari sun ziyarci Sanusi ranar Talata.

Tawagar ƴan kasuwar karƙashin jagorancin kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar Kano, Adamu Aliyu Kibiya, sun ziyarci Sarki Sanusi II a fadar Kofar Kudu.

Ƴan kasuwar sun yi mubaya'a tare da tabbatar da goyon bayansu ga Sarki Muhammadu Sanusi II.

Tun ranar Lahadin da ta gabata ne dai Sarki Sanusi ke karbar baki masu zuwa domin yin mubaya’a, ciki har da hakimai da masu rike da mukaman sarauta 40.

Bincike ya nuna cewa kungiyoyin ’yan banga da mafarauta (Yan Tauri) na ci gaba gadi da sa ido a fadar.

Haka nan an ga jami’an hukumar tsaron farin kaya DSS 5 a kofar shiga daya daga cikin ofisoshin sarkin da ke Gidan Rumfa.

Dakkawan kudancin Kano sun ɗauki matsaya

A wani rahoton kuma masu ruwa da tsaki a yankin masarautun Gaya, Karaye da Rano sun yi fatali da rushe masarautu biyar da Abba Yusuf ya yi a Kano.

Sun buƙaci gwamnatin Kano da majalisar dokoki su bi umarnin babbar kotun tarayya wadda ta hana rushe masarautun.

Asali: Legit.ng

People are also reading