Home Back

Rundunar Sojin Najeriya Ta Dauki Matakin Gaggawa Kan Cin Zarafin Farar Hula a Legas

legit.ng 2024/7/3
  • Rundunar sojin Najeriya ta fusata biyo bayan zargin cin fuska da jami'anta suka yi wa fararen hula a wata makaranta a jihar Legas
  • Hafsun sojojin ƙasa, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne ya ba da umurnin ɗaukan matakin kamar yadda rahotanni suka nuna
  • Kungiyar manyan ma'aikatan gwamnati ta kasa (ASCSN) ce ta shigar da korafi biyo bayan zargin jami'an soji da aikata ba daidai ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Rundunar sojin Najeriya ta ba da umurnin gaggawa domin yin bincike kan zargin jami'anta da muzgunawa fararen hula.

Hafsun sojojin ƙasan Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne ya ba da umurnin tare da kira a yi adalci a ciki.

Sojojin Najeriya
Za a binciki sojojin da suka ci zarafin fararen hula a Legas. Hoto: HQ Nigerian Army Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne cikin wani sako da jami'in yada labaran rundunar ya wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ASCSN ta shigar da korafi

Kungiyar manya ma'aikatan gwamnati ta kasa (ASCSN) ta shigar da korafi ga rundunar sojin Najeriya bisa zargin cin zarafin ma'aikata.

Kungiyar ASCSN ta ce jami'an soji sun ci zarafin ma'aikata a makarantar sojoji da ke Iyana Ipaja a jihar Legas.

Rundunar soji za ta yi bincike

Biyo bayan korafin, Hafsun sojojin ƙasa, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya umurci shugaban makarantar ya gaggauta yin bincike kan lamarin.

Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya ce bincike zai gano gaskiya tare da lura da korafin da kungiyar ASCSN ta shigar.

Haka ba zai kara faruwa ba

Rundunar sojin Najeriya ta ce ma'aikatan da ba sojoji ba suna taka muhimmiyar rawa a harkar gudanar da makarantar.

Saboda haka ta ce za a yi binciken ne domin daukan matakin da zai hana sake faruwar cin zarafin wani ma'aikaci da ba soja ba.

Sojoji sun gargadi Sunday Igboho

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta gargadi Sunday Adeyemo kan irin kalaman da ya ke yi tun bayan dawowa Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta ce idan har abin da ya fada zai inganta tsaron kasar babu matsala amma sabanin haka kuma ya kauce layi.

Asali: Legit.ng

People are also reading