Home Back

Bidiyon da ke yawo an sokawa wani matashi Wuƙa a ciki a Ɗorayi ba gaskiya ba ne – Cewar ƴan sandan Kano

dalafmkano.com 2024/5/17

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta umarci baturan ƴan sanda a faɗin jihar Kano, da su riƙe duk wanda yazo karɓar belin ƴan fashi da makamin da ta kama na yankin Ɗorayi ƙarama.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Muhammad Usaini Gumele, ne ya bayyana hakan yayin taron magance matsalar daba dake faruwa a unguwar Dorayi Karama, da ya gudana da yammacin yau Alhamis.

Rundunar ƴan sandan ta jihar Kano ta kuma musanta wani bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta dake nuna cewar ana cakawa wani matashi wuka a unguwar ta Dorayi Karama, wanda ta ce bidiyon ba gaskiya bane.

A nasa jawabin kwamnadan bijilanti na jihar Kano Shehu Muhammad Rabi’u, cewa ya yi masu bibiyar waɗanda aka kama da zargin aikata laifuka kamin kammala bincike na cikin dalilin karuwar matsalar daba da fashi da makami a lokuta da dama.

Da yake nasa jawabin dagacin Dorayi Karama Shehu Umar Sani, ya ce za su bayar da duk wani hadin kai da rundunar ƴan sandan take buƙata wajen kamo duk wanda yake cikin ƴan daba ko fashi da makami.

Rundunar ƴan sandan ta kuma ƙara da cewa za ta fara aikin kota kwana a yankin na Ɗorayi, tare da neman haɗin kan sauran jami’an tsaro dan tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin da ma na jihar Kano baki ɗaya.

A ƴan tsakanin nan ne dai wasu rukunin matasa suka addabi al’ummar yankin na Ɗorayi, inda aka zargi sun yi kan mai uwa dawabi akan mutane da sara, tare da ƙwacen wayoyin al’umma, bayyana da aka ce sun rarraba takardu kan cewar za su kai harin tare da hana yin sallar Tarawi.

People are also reading