Home Back

An yi belin shugaban shafin WikiLeaks

dw.com 4 days ago
Julian Assange
Julian Assange shugaban Wikileaks

Kungiyoyin kare hakki na 'yancin albakacin baki a sassan duniya daban-daban sun yi maraba da sakin dan jaridar nan na Austireliya kuma shugaban WikiLeaks Julian Assange daga gidan kasa a Birtaniya.

Kungiyoyin da suka hada da Committee to Protect Journalists ce tsare Asange din da aka yi na tsawon lokaci wani tarnaki ne babba ga aikin jarida da kuma su kansu 'yan jarida da ke aiki a kasashen duniya.

Rahotannin da ke shigo na cewar tuni Assange ya bar Birtaniya, kuma sun ce zai gurfana ne gaban kuliya a gobe Laraba don amsa tuhuma da ake yi masa kan zargin kwarmata bayanan sirrin Amirka. Dan jaridar ya shafe kimanin shekaru 14 a gidan kason Birtaniya, inda aka yi ta tika-tirka kan zarge-zargen da Amirka take yi masa na hada kai da wani jami'in asirin Amirka Chelsea Manning da kuma yunkuri na wallafa wasu bayanan sirrin kasar.

People are also reading