Home Back

IMF Ta Bayyana Dalilinta Na Neman Gwamnati Ta Janye Tallafin Lantarki

leadership.ng 2024/6/18
IMF Ta Bayyana Dalilinta Na Neman Gwamnati Ta Janye Tallafin Lantarki

Hukumar Lamuni ta Duniya IMF ta sanar da dalilita na gargadin Nijeriya a kan bukatar da gaggauta janye tallafin man fetur da na wutar lantarki in har tana son samun daidaito a bunkasar tattalin arziki.

A rahoton da ta wallafa kwanan nan, IMF ta ce, tallafin da ake bayarwa zai cinye kashi 3 na kudaden shigar kasar a shekarar 2024 ba kamar yadda ya kasance kashi 1 a shekarar data gabata ba. A kan haka IMF ta nemi gwamnati ta dakatar da bayar da tallafin gaba daya tare da karkatar da kudaden zuwa wasu bangarori na jin dadin al’umma da kuma rage basukan da aka bin kasar daga kasashen waje.

Idan za a iya tunawa, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sanar da janye tallafin man fetur a ranar da aka ratsar da shi a mastayin shugaban kasa, 29 ga watan Mayu 2023.

IMF ta kuma lura da cewa ba a samar da tsarin tallafi ba al’umma ba sakamakon janye tallafin an kuma dakatar da bayar da tallafin sakamakon sama da fadi da wasu jami’an gwamnati suka yi, wanda da kuma hauhawar farashin kayan masarufin sun kara tsadar rayuwa a Nijeriya fiye da duk wani lokaci da aka sani.”

Hukumar ta kuma bayyana yadda aka samu karin farashin wutar lantarki musamman da kusan kashi 15 na masu amfani da wutar wanda suka kai kimanin miliyan 15, wanda hakan ya jawo cecekuce a fadin kasa.

A yayin da al’umma Nijeriya ke kira da a soke karin da aka yi daga N68, a kan kilowatt daya zuwa N206.80 a kan liwatta daya. Sai dai IMF ta ce, karin kudin da aka yi zai taimaka wajen karin kudin shiga na kasa da kashi 0.1.

Daga nan IMF ta nemi gwamnati da ta gaggauta janye tallafin da zaran an daidaita farashin kayan nmasarufi don shi ne mafita ga matsalar tattalin arzikin da kasa ke fuskanta”, in ji ta.

Tuni da kungiyoyin kwadago dana masu fafutukar rajin kwato hakkin bil adam suka nuna kin amincewasu a kan wannan mastaya na IMF, suna masu nuni da cewa, yaushe za a ce wata kungiya daga kasashen waje ne za ta rika ba gwamnatin tarayya umarnin abin da ya kamata ta yi dangane da jin dadin al’ummata, a akan haka suka yi kira ga ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu ya gaggauta dawo da farashin yadda yake a da.

People are also reading