Home Back

Isra'ila ta tsagaita wuta na tsawon sa'o'i 11 a Gaza

dw.com 2024/6/26
Isra'ila ta tsagaita wuta na tsawon 'yan sa'o'i a Gaza
Isra'ila ta tsagaita wuta na tsawon 'yan sa'o'i a Gaza

A cikin sanarwar da suka fidda sojojin na Isra'ila sun ce za a dakatar da yaki daga takwas na safiya zuwa karfe bakwai na maraicen Lahadin nan a mashigin Kerem Shalom da kudancin Gaza zuwa mararrabar hanya ta Salahaddine.

Kazalika Isra'ilar ta sanar da mutuwar sojojinta 11 a yayin gumurzu da kuma fashewar wasu abubuwa a ranar Asabar a zirin na Gaza inda yaki ke daukar dumi yau sama da watanni takwas. 

Wannan mataki dai ya biyo bayan tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya da kuma wasu kungiyoyin na kasa da kasa suka yi da mahukuntan Isra'ila kan samun karin kayan agaji da za su shiga yanki Falasdinu da ke fama da barazanar yunwa.

A daya gefe kuma matakin zai bai wa al'ummar Gaza dama domin sararawa musamman a daidai wannan lokaci da ake bukukuwan babbar Sallah.

People are also reading