Dan Majalisar Wakilai da Ya Kai Wa Gwamnan PDP Ziyara Ya Shiga Matsala, Ana Tuhumarsa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar wakilai ta shirya tuhumar wani dan majalisa, Hon. Ikenga Ugochinyere, mamba mai wakiltar mazabar Ideato na jihar Imo.
A zamanta na ranar Alhamis, majalisar ta mika Hon. Ugochinyere ga kwamitin da'a da gata domin tuhumarsa kan ziyarar da ya kai wa gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara.
Dan majalisa daga jihar Filato, Hon. Yusuf Gagdi ne ya gabatar da bukatar inda ya zargi Hon. Ugochinyere da 'bata suna majalisar', in ji rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan da ya gabata, Hon. Ugochinyere ya jagoranci mambobin majalisar wakilai sama da 50 zuwa bikin cika shekara daya na gwamnatin Fubara a Port Harcourt, babban birnin Rivers.
Hon. Ugochinyere, dan jam’iyyar PDP ne mai goyon bayan Fubara kuma ya bayyana kansa a matsayin mai magana da yawun ‘yan majalisar adawa 60.
HA ranar 4 ga watan Yuni, Hon. Ugochinyere ya wallafa bidiyon ziyarar da suka kai a shafinsa na X.Hon
Yayin da yake gabatar da bukatar, Gagdi ya ce an keta alfarmarsa a matsayinsa na dan majalisar dokoki saboda Ugochinyere ya ce ‘yan majalisar sun kai ziyarar a madadin majalisar.
Hon. Gagdi ya ce bayan ziyarar da ya kai wa Fubara, Hon. Ugochinyere ya fitar da wata sanarwa wadda ta nuna cewa ‘yan majalisar sun wakilci majalisar wakilai a ziyarar.
“Ba laifi ba ne a kai ziyarar nuna goyon baya, amma ba daidai ba ne a nuna cewa tawagar na wakiltar kafatin majalisar. Ina fatan majalisar za ta duba wannan lamari."
- In ji Hon. Gagdi.
Mataimakin kakakin majalisar, Ben Kalu wanda ya jagoranci zaman ya mika batun ga kwamitin da'a da kuma gata.
A wani labarin, mun ruwaito cewa NNPP a Edo ta dakatar da ɗan takarar ta na gwamnan jihar, Azemhe Ezena kan zargin kin biyayya ga jam'iyyar.
Wannan dakatarwar wadda Azemhe Ezena ya yi watsi da ita na zuwa ne ana saura watanni uku a yi zaben gwamnan jihar Edo.
Asali: Legit.ng